Shalkwatar tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta tabbatar da mutuwar ’yan ta’adda 34 da sojoji shida a wani harin da aka kai sansanin soji da ke Sabon Gari, ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno.
Daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa.
- Hadimin Gwamnan Kano Ya Rasu Kwana Ɗaya Bayan Rantsar Da Shi
- NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa
Ya ce sun boye sunayen sojojin da suka mutu har sai an sanar da iyalansu.
Manjo Janar Buba ya ce harin ya biyo bayan yunƙurin ramuwar gayya da ’yan ta’adda suka yi bayan kashe kwamandansu a baya.
Sai dai, sojoji sun daƙile harin yayin da suke dawowa sansaninsu.
Ya ƙara da cewa tawagar haɗin gwiwa ta sojoji, ’yan banga, da Civilian Joint Task Force (CJTF) sun isa wurin da lamarin ya faru, inda suka yi nasarar fatattaki ’yan ta’addan.
Duk da fashewar wani abu da ya raunata kwamandan ’yan banga, sun isa wurin cikin lokaci.
Rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI ita ma ta kai wa ’yan ta’addan farmaki, inda suka tsere.
Manjo Janar Buba ya jaddada cewa rundunar sojojin Nijeriya tana kan bakanta na kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar.
Ya kuma tabbatar da cewa za su ci gaba da jajircewa har sai sun tabbatar da zaman lafiya.