A jiya Talata, manema labarai sun zanta da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi bayan ganawarsa da shugaban kasar Jamhuriyar Kongo, Denis Sassou Nguesso.
Da aka tambaye shi game da shirye-shiryen da kasar Sin da Jamhuriyar Kongo suke da su a matsayin jagororin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wajen aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin da aka gudanar a Beijing bara, Wang wanda har ila yau mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin koli na Jamiyyar Kwaminis ta Sin, ya ba da amsar cewa, dandalin FOCAC ya taka muhimmiyar rawa wajen daukaka ci gaban Afirka tare da kyautata jin dadin mutanen yankin.
- JKS Ta Yi Kira Da A Karfafa Gwiwa Da Jajircewa Wajen Yaki Da Cin Hanci Da Karbar Rashawa
- An Yi Wa ‘Yansanda 110 Ƙarin Girma A Adamawa
Wang ya zayyano wasu muhimman abubuwa guda uku da za a yi laakari da su wajen aiwatar da sakamakon taron bayan tuntubar juna a tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata.
Da farko, Wang ya ce za a karfafa daidaita dabarun samar da ci gaba da musayar fikira da basirar iya shugabanci a tsakanin juna, da zurfafa amfani da hikimomi da sassan cin moriyar juna domin fadada alakokin kasar Sin da Afirka.
Abu na biyu da za a mayar da hankali a kai in ji Wang Yi, shi ne ci gaba da kara kaimin yaukaka zumunci da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, da kara fito da hanyoyi mafiya dacewa da alakar kasa da kasa, da zama abin koyi ta fuskar hadin gwiwa a tsakanin Afirka da sauran yankunan duniya.
Kana na uku, shi ne gano alkiblar da ta fi dacewa a dosa da kuma muhimman ayyukan ci gaba da za a fi dora fifiko a kai, tare da habaka matakan zuba jari da cinikayya tsakanin Sin da Afirka domin samar wa yankin na Afirka da kasuwar hada-hada mai girma, da aiki da fasahohin zamani da ci gaba da zuba jarin zamanantar da yankin ba tare da tangarda ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)