Ba karamar damuwa ce, musamman ma ga masu kishin Nijeriya,idan aka yi la’akari da sanarwar da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta yi na cewar, ta lalata jabun Magununa da kudinsu ya kai sama da Naira biliyan 120, a cikin watannin shida da suka gabata kacal.
Wannan adadin, ya kai na yawan jabun magungunan da Hukumar ta kwace ne daga watannin Oktoba zuwa Disamba na 2024.
- Fashewar Bam Ya Kashe Dalibi ɗaya, Ya Jikkata 4 Abuja
- Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja
Adadin, ya jefa matukar fargaba a zukatan al’ummar kasa da ke yin amfani da magungunan wajen nemawa kansu lafiya, musamman ma irin wannan dimbin magungunan na jabun da ake shigowa da su cikin Nijeriya, aka kuma wucewa da su, kai tsaye, zuwa kasuwannin kasar domin sayarwa jama’a.
Hakan ya kara fallasa yadda yanayin iyakokin kasar suka kasance a matsayin kara zube wajen shigo da nau’oin jabun kaya cikin kasar, ba tare da sa idon masu kula da iyakokin kamar yadda ya kamata ba.
Kazalika ma, kwace irin wadannan jabun kayan, da bata garin masu sayar da magungunan na jabu ke yi domin samun kazamar riba, hakan na kuma kara jefa marasa lafiyar, a cikin wani mummunan yanayi na rashin lafiyar da suke fuskanta.
A samamen da Hukumar ta kai a manyan Shagunan sayar da jabun magungunan da ke a kamar Legas, Fatakwal, Abiya da kuma Abuja, ta bankado irin wadannan jabun magungunan da kudinsu ya kai na sama da biliyoyin Naira.
Wannan matsalar, tana kara haifar da kalubale ga tsarin kiwon lafiyar kasar da kuma fannin tattalin arziki.
Bugu da kari, Hukumar ta kuma bankado jabun lemon Kwalba a wajen baje kolin kaya da ke jihar Legas, tare da kuma garkame wasu masana’antun da suke sarrafa Shinkafar da ta lalace da kudinta ya kai kimanin Naira biliyan biyar a jihar Nasarawa, wanda hakan ya nuna irin babbar ta’asar da masu son kazamar ribar, suke aikatawa.
Wannan gano jabun kayan, ya zo daidai da lokacin da ake yin nazari kan yawan kudaden da marasa lafiya suka kashe, wajen sayen magunguna.
Shugabar Hukumar ta kasa Farfesa Mojisola Adeyeye ta alakanta irin wadannan masu sayar da jabun magungunan domin samun kazamar riba, a matsayin makasa.
Hukumar ta kuma kulle manyan Shaguna 150 a kasuwar Eziukwu, da ke a yankin Aba da ake sayar da jabun Lemon Kwalba.
Kazalika ma, sayar da irin wannan jabun kayan yana hanawa Gwamnati samun kudaden shiga, tare da kuma da zubar da mutuncin Nijeriya, a idon kasuwar duniya, inda kuma a yayin da irin wadannan jabun magungunan suka cike kasuwa, ke haifar da gasa a tsakanin ainihin masu sarrafa magungunan na gaske, tare da haifar masu da asara da durkushewar kasuwancinsu.
Bisa ga namu ra’ayin, a yayin da hukumar NAFDAC ke kara jajircewa wajen yakar irin wadancan mutanen masu sarrafa jabun magungunan, ta canci yabo.
Yadda aka lalata jabun kayan da kudinsu su ka kai na kimanin Naira biliyan 120, hakan ya nuna cewa, akwai gazawa ta magance matsalar.
Kazalika, hakan ya janyo bijero da tambaya a zukatan ‘yan Nijeriya, na rashin sa ido a iyakokin kasar.
Ya zama wajibi ne a dauki matakai daban daban domin kawo karshen ita wannan matsalar.
daya daga cikin matakan, na farko, ya kamata a kulla hadaka mai karfi a tsakanin NAFDAC da jami’an Hukumar Kwastam da kuma sauran Hukumomin tsaro, don a dakile shigo da jabun kaya cikin kasar.
Abu na biyu kuma shi ne, a rinka hukunta su batagarin da suke sarrafa kayan jabun, don hakan ya zama darasi ga sauran masu tunanin aikata irin haka a nan gaba.
Kuma ya kamata a rinka yin amfani da kimiyyar zamani wajen dakile shigo da kayan na jabu da kuma samar da na’urorin zamani, da za su rinka tantance, kayan da ake shigowa da su.
Kazalika ma, ya zama wajbi, Hukumar NAFDAC, ta kara kaimi wajen ilimantarwa da fadakar da ‘yan kasar kan sayen kaya masu inganci,don haka akwai bukatar a samar da shirye-shiyen ilmantarwa a makarantu da hakanan a cikin al’umomi, kan yadda za a iya saurin gane jabun kaya a kuma kai rahoto, ga mahukuntan kasar nan.
Akwai matukar bukatar sahihan kamfanoni masu zaman kansu da masu saye da sayarwa, suma su kara jan damara, wajen yakar masu sarrafa kayan jabu, musamman ma ta hanyar yin amfani da kimiyyar zamani, don gano jabun kaya.
Ya kuma kamata su rika yin aiki kafada – kafada da Hukumomi a kasar nan, domin kare kayan da suke sarrafawa da kuma kare lafiyar, masu sayen kayan domin su yi amfani da su.
Idan har ba a kawo karshen wadannan matsalolin da aka zayyana a sama ba, za ci gaba da komawa ‘yar gidan jiya.