Wata mummunar gobara ta yi ajalin wata mata mai suna Jumai Sunday, ‘yar shekara 24 tare da ɗanta, Nasir Rabiu, mai shekaru 6 inda ta ƙonesu ƙurmus har lahira.
Lamarin ya faru ne a wani gida da ke kasuwar kayan ɗaki ta Kugbo da ke Ƙaramar Hukumar AMAC, na babban birnin tarayya Abuja, a daren ranar Laraba, yayin da suke zaune a ɗaki tare da ɗanta ɗaya.
- NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 7 Da Ake Zargi Da Laifin Sace Murafan Kwalbati A Abuja
- Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja
Duk da ƙoƙarin jami’an kashe gobara na shawo kan wutar sanda ta ƙonesu, wanda maƙwabta ne da masu zuwa jaje suka gano gawarwakinsu yayin gyara kadarorin da gobarar ta lalata.
Rundunar ’yansanda ta tabbatar da faruwar lamarin kammar yadda jami’i mai kula da yankin Karu, Lakur Langyi, ya shaida cewa sun samu kiran gaggawa cikin dare daga yankin game da batun.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, amma suna gudanar da sahihin bincike domin ganowa da zummar kiyayewa a gaba.