Gwamnatin Najeriya ta karɓi dala miliyan $52.88 da aka kwato daga dukiyoyin Galactica da aka danganta da tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, daga Amurka.
Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi, ya bayyana hakan a wajen rattaba hannu kan yarjejeniyar dukiyoyin da aka kwato tsakanin Najeriya da Amurka a Abuja ranar Juma’a. Ya ce dala miliyan $50 za a yi amfani da su wajen samar da hasken wuta a karkara ta hanyar haɗin gwuiwa da Bankin Duniya, yayin da sauran dala miliyan $2 za a ba Cibiyar Shari’a ta Duniya don faɗaɗa tsarin shari’a da yaƙi da cin hanci.
Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya yi kira da a tabbatar da cewa Ma’aikatar Shari’a ta yi amfani da kudaden da aka kwato ta yadda za su amfani al’ummar Nijeriya, yana mai bayyana wannan a matsayin ci gaba mai muhimmanci wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.