Shafin hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ya shafe makonni uku a rufe tun bayan da masu kutse suka kutsa cikinsa.
Maziyarta shafin ko a ranar Litinin sun laluvo, amma sun samu shafin baya aiki. Wannan na zuwa ne yayin da ake sa ran hukumar za ta fitar da rahoton hauhawar farashin kayayyaki na watan Disamba a ranar 15 ga watan Janairun 2025.
- Za a Fara Kera Motoci Da Babura Masu Amfani Da Lantarki A Kano
- Gandunje Ya Haifar Da Babbar Matsala Ga Ci Gaban Al’ummar Kano – Gwamna Abba
Rahotanni sun bayyana cewar a ranar 18 ga watan Disamban 2024 ne hukumar NBS ta tabbatar da cewa an yi kutse cikin shafin yanar gizo dinta.
NBS ta sha alwashin kwato ikon shafinta, wanda shi ne ya kasance dandamalin samun sahihin kididdiga da kuma bayanai.
Wannan farmakin da aka yi wa shafin na zuwa ne a lokacin da NBS ta ware naira miliyan 35 domin tsaron yanar gizo a ciki kasafin kudinta na 2025 da ya kai naira biliyan 9.85.
Shafin hukumar ya samu masu kutsen ne bayan da ya fitar da rahoton binciken tsaro da ya yi nuni da cewa ‘yan Nijeriya sun biya kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da yawansa ya kai naira tiriliyan 2.3 a cikin watanni 12 wato shekara guda, kuma kaso 65 na magidanta sun gamu da illar garkuwa da mutane.