Sojojin Nijeriya na bataliya ta 195 sun ce sun kama mutane bakwai masu jigilar kai wa mayakan Boko Haram da masu satar mutane kayayyaki.
Hukumomin sojin sun ce sun yi nasarar kama mutanen ne da suka hada da Hadiza Ali da Kelo Abba da Mariam Aji da Kamsilum Ali da Ngubdo Modu da Abiso Lawan da wasu, a wajen babban birnin jihar Borno, Maiduguri.
- ‘An Kashe Mayakan Boko Haram Da Yawa A Wani Hari Da Sojoji Suka Dakile A Neja’
- Luguden Ruwan Wuta Ya Kashe Kwamandan Boko Haram A Borno
Wannan na kunshe ne a wasu bayanan sirri da wani masanin harkokin tsaro Zagazola Makama, ya samu tare da bayyanawa jaridar.
Rahoton ya nuna cewa an kama mutanen ne da tarin kayayyaki da suka hada da man fetur da gidan sauro da taliya a yayin wani bincike, a kan hanyarsu ta kai wa ‘yan Boko Haram kayayyakin.
”Sojojin sun zargi mutanen ne bayan da suka ga garin-kwaki mai yawan gaske an boye a cikin galan-galan da kuma karkashin motar da mutanen ke ciki.” kamar yadda rahoton ya nuna.
Ya kara da cewa, ” Bayan an tsananta bincike ne sai matan suka tabbatar wa da sojojin cewa su ‘yan Boko Haram ne da ke aiki a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Garejin Muna da Mafa da Dikwa, inda mayakansu ke zaune a yankin bakin ruwa na Boboshe da Gulumba a karamar hukumar Dikwa ta jihar ta Borno.
A sanadiyyar wannan kamen ne kamar yadda bayanan suka nuna sojojin suka fadada bincike abin da ya kai su ga kashe dan Boko Haram daya da kona wata babbar mota daya suka kuma kubutar da mutum biyar da aka sace a wani sansani.