Ana jimamin kisan wata budurwa mai suna Salome Adaidu, mai shekara 24, wadda ake zargin saurayinta Timileyin da kashe ta a Jihar Nasarawa.
Ƴan sanda sun damƙe Timileyin ɗauke da kan Salome cikin jaka a ranar Lahadi, 12 ga Janairu, a kusa da wata coci.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- Sin Za Ta Dauki Mataki A Kan Tankunkumin Fasahar AI Da Amurka Ta Kakaba
Bayan bincike, an gano gawar Salome a gidansa, a cikin buhu, bayan an daddatsa ta.
Rahotanni sun ce ɗan acaɓa ne ya lura da jini na diga daga jakar Timileyin, wanda ya jawo hankalin mutane suka taru suka damƙe shi, kafin a miƙa shi ga ƴansanda.
Mahaifiyar Salome ta yanke jiki ta faɗi da jin labarin, kasancewar ba ta jima da rasa mijinta ba.
Wannan lamarin ya girgiza jama’a, inda suke Allah-wadai da kisan da aka yi wa Salome.
Ƴansanda na ci gaba da bincike kan alaƙar Timileyin da marigayiyar.