Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.80 a watan Disamban 2024, daga kashi 34.60 a watan Nuwamba.
Farashin kayan abinci ya kuma ƙaru zuwa kashi 39.84 idan aka kwatanta da kashi 33.93 a Disamban 2023, sakamakon tashin farashin kayayyaki kamar doya, dankali mai, da giya.
- Karramawa: Ma’aikatan Kano Sun Yaba Wa Jagorancin Gwamna Abba Na Tausayi
- Afrika Na Da Damar Kawowa Kanta Ci Gaba – Tinubu
Hukumar ta ce wannan ƙarin ya faru ne saboda ƙaruwar buƙatar kayayyaki a yayin bukukuwan Disamba.
Duk da haka, ƙarin farashin daga wata zuwa wata ya ragu zuwa kashi 2.44 a Disamba, daga kashi 2.64 a Nuwamba.
Idan aka kwatanta da Disamban 2023, an samu ƙarin kashi 5.87 a farashin kayayyaki gaba ɗaya, wanda ke nuna tashin farashin kayayyaki cikin shekara ɗaya.