Masu iya magana suna cewa, Jumma’ar da za ta yi kyau,tun daga Laraba ake gane ta, wannan maganar,ta yi daidai, idan aka yi la’akari da yadda alkalumman yanayin tattalin arziki na 2024 suka nuna, ya kasance, inda hakan ya zama wata ‘yar manuniya ce kan yanayin da Nijeriya za ta kasance, a 2025.
Misali yadda a 2024 wanda ta gabata, matsin rayuwa ya janyo wasu talakawan kasar suka rasa rayukansu, a yayin da aka yi turmutsin rabon kayan tallafin abinci, hakan ne ya nuna a zahirin gaskiya, ko shakka babu lamarin ya kai makura.
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
- Kotu Ta Ɗaure Wasu Mutane 4 Da Ake Zargi Da Satar Birkin Jirgin Sama Guda 80 A Kano
Cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya da ke kan mulki ta yi, da kuma karyewar darajar Naira,hakan ne ya kara janyo wata babbar barazana da kuma kara jefa talakawan Nijeriya, a cikin kangin talauci.
Biyo bayan cire tallafin man, farashin kayan masarufi da yadda al’ummar kasar, ke gudanar da ayyukansu na yau da kullum, sun kara hauhawa, tare da kuma janyo hauhawar farashin kaya da kara haifar da rashin ayyukan yi.
Kazalika ma,lamarin ya janyo wasu kamfanoni da dama da suke gudanar da ayyukansu,ko dai sun fice daga kasar, ko kuma sun garkame kamfanonin, musamman ma saboda karyewar darajar Naira da kuma tsadar gudanar da ayyukansu.
Wannan kalubalen, ya janyo Nijeriya ta yi asarar dimbin kamfanonin da suka zuba jarinsu a kasar wanda ya kai na yawan biliyoyin dala.
Bugu da kari kuma, sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta kirkiro da su, alamu ne da suke nuna cewa, ana samun jinkiri wajen kokarin da gwamnatin ke yi, na cike gibin, duk da kokarin da ake yi, na samo masu zuba hannun jari na kai tsaye, daga ketare.
Misali, wani fitaccen kamfanin hada magunguna na kasa da kasa wato GladoSmithKline, a watan Agusta ne 2023 ne, ya bayyana dakatar da gudanar da ayyukansa, a Nijeriya.
Wannan lamarin ya nuna cewa, sai dai Nijeriya ta koma shigo da magunguna daga ketare, inda kuma za ta rinka kashe dimbin kudade,wajen shigo da magungunan da kamfanin ke sarrafawa zuwa cikin kasar.
Kasancewar Nijeriya na kan matakin da ‘yan kasar ba wuya sun kamu da rashin lafiya, musamman ma saboda karancin abinci mai gina jiki, lamarin da zai iya kara munana.
Kazalika ma, kamfanin P&G, shi ma ya tattara kayansa ya bar kasar, saboda kalubalen samun Dalar Amurka a Nijeriya.
A farkon watanni shida na 2024, sama da kamfanoni biyar ne suka fice daga Nijeriya, saboda rashin samar da kyakkyawan yanayin yin kasuwanci.
Kamfanonin su ne; Microsoft, Total Energies,PZ Cussons Nigeria Plc da dai sauransu, inda suka koma wasu kasashe da ke makwabtaka da Nijeriya, da suke da kyakkyawan yanayi na yin kasuwanci.
Ficewar wadannan kamfanonin, yana kara nuna yadda darajar Naira ta kai ga munzalin karyewar darajar ta wanda kuma hakan zai janyo nakasu ga bangaren zuba hannun jari a kasar.
Hakazalika, a wani rahoton kwanan baya da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar, ya nuna yadda hauhawar farashin kaya, a watan Nuwambar 2024, a kasa ya kai matakin kashi 34.6.
Haka hauhawar farashin kayan abinci, ya kai kashi 40, inda hakan ya kara jefa talakawan Nijeriya, a cikin kangin talauci.
A cewar alkalumman Hukumar Kula da Farashin Kaya ta kasa CPI rahoton Hukumar kula da harkokin kididdiga ta kasa ya nuna cewa, lamarin ya ci gaba da karuwa ne har zuwa sama da watanni uku, inda a watan Nuwamba ya karu da da kashi 0.72, idan aka kwatanta da yadda na watan Okutobar 2024 yake.
Kazalika, wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar da ya nuna yadda sama da ‘yan Nijeriya miliyan 14, suka fada a cikin kangin talauci a cikin watanni 18.
Lamarin abin takaici ne la’akari da yadda ‘yan Nijeriya sama da miliayn 133 a shekarar 2024, suke ci gaba da fuskantar talauci.
Domin a lalubo da mafita kan wannan kalubalen, gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudi ga majalisar kasar na Naira tiriliyan 47.9.
Sai dai kuma, ta hanyar kasafin kudin, gwamnatin Tinubu, ta ayyana nufin samar da sauki kan abubuwan da aka fi bukata na yau da kullum,ciki har da rage yawan hauhawar farashin kaya daga kashi 34.6, zuwa kashi 15, tare da farfado da darajar Naira akalla daga Naira 1,700 zuwa kan duk Dala daya 1,500.
Sai dai, akwai gibin da ya kai sama da Naira tiriliyan 13 a cikin kasafin kudin, wanda hakan ne,ya ke haifar da fargaba,dalilin hakan ne ya sa dole ne gwamnatin, ta ciwo bashi, domin ta cike gibin a cikin kasafin kudin.
Kamar yadda wannan Jaridar ta ruwaito a ranar 30 ga watan Disambar 2024, masu fashin baki da kwararru a fannin tattalin arziki, suna da yakin cewa,idan aka farfado da darajar Naira aka rage farashin man fetur a 2025, aka kara karfafa samar da kudaden musaya na waje, da kuma rage shigo mai,za a samu sauki.
Wannan yakinin na su, ya zo daidai da ake kara samar da mai a kasar ta hayar sarrafa shi a cikin kasar, wanda hakan zai samar da sauki a kan kudin kasar.
Kazalika ma, wannan samun ci gaban da aka samar, zai daidai ta, farashin mai.
A sakonsa na sabuwar shekarar 2025, Shugaba Tinubu ya mayar da hankali ne, kan rage hauhawar farashi daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 a karshen 2025.
Sai dai kuma,furucin na sa ya nuna aukwar lamarin a zahiri, idan aka yi la’akari da yadda tattalin arzikin kasar, ke ci gaba da fuskantar kalubale.
Kasafin kudin na Naira tiriliyan 47.9 na tare da gibin da ya kai na sama da Naira tirliyan 13, wanda hakan ya sa manyan tamboyi, fiye da bayar da amsa, game da daburun da gwamnatin za tayi amfani da su.
Yakinin gwamnatin game da daga darajar Naira daga Naira 1,700 a kan duk dala daya 1,500, hakan ya nuna ana sa rai na samun karuwa a musayar kudaden waje da kuma rage shigo da shi.