Yayin da zaben shekarar 2027 ke kara kunno kai, akwai zargi mai karfi na sauya sheka a tsakanin gwamnonin adawa guda 5 kafin zaben 2027, kamar yadda binciken LEADERSHIP ya tabbatar.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa gwamnonin Abiya, Aled Otti, da na Inugu, Peter Mbah da na Delta, Sheriff Oborebwori da na Ribas, Siminalayi Fubara da na Akwa Ibom, Umoh Eno, sun tattaunawa kan shirinsu na yin watsi da jam’iyyunsu tare da sauya sheka zuwa APC mai mulki.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan YaÉ—a Labarai
- Hamas Ta Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Isra’ila
Yayin da Mbah, Fubara, Eno, Oborebwori na cikin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Otti na jam’iyyar LP ne. Dukkanin jam’iyyun biyu a fama da rikice-rikicen cikin gida bayan kammala zaben 2023.
Wasu majiyoyi sun shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu daga cikin gwamnonin ana masu matsinlamba don su koma jam’iyyar APC mai mulki, wasu kuma na ganin cewa, bisa la’akari da rashin zaman lafiya a cikin jam’iyyarsu, a shirye suke su shiga wani jam’iyya da zai kara musu damar samun wa’adi na biyu.
Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya a shekarar 1999, gwamnoni sama da 20 ne suka bar jam’iyyunsu na siyasa. Jihohin da suka fi yawan gwamnonin da suka sauya sheka sun hada da Sakkwato, Imo, Abiya da Adamawa.
A Sakkwato, gwamnoni uku suka sauya sheka a jam’iyyunsu na asali, yayin da gwamnoni biyu masu ci a Imo da Abiya da Zamfara da Adamawa suka sauya sheka.
Sai dai kuma maganar ficewa daga jam’iyyar gwamnan Abiya ya kara ta’azzara ne yayin kaddamar da ginin filin jirgin saman Abiya, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa gwamnan Abiya zai koma APC.
Haka kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya matsa wa Otti lamba ya koma APC.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa kawo yanzu ‘yan majalisar wakilai na jam’iyyar LP sama da 5 ne suka koma jam’iyyar APC.
A Jihar Ribas, Gwamna Fubara ya yi amfani da jam’iyyar APP wajen zaben kananan hukumomi, biyo bayan gazawar da ya yi wajen kwace tsarin PDP daga hannun Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ci gaba da tattaunawa cewa zai iya ficewa daga PDP kafin zaben 2027.
Kusancin gwamnan Jihar Akwa Ibom, Eno da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, kasancewarsa daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC na kasa, ya iya yin tasiri wajen janwo ra’ayin gwamnan zuwa jam’iyya mai mulki.
A Inugu, rikicin cikin gida da ke kawo cikas a cikin jam’iyyar PDP a matakin kasa na iya sa gwamnan ya karkatar da hankalinsa zuwa wata jam’iyya.
Shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Delta, karkashin jagorancin kungiyar shugabannin PDP, sun tofa albarkacin bakinsu game da soyayyar Oborebwori da shugabannin APC. Shugabannin jam’iyyar, wato Mista Theophilus Ekiyor, Mista Ochuko Oghenekome, da Mista Ezekiel Chukwudi, a wata budaddiyar wasika, sun zargi gwamnan da yin alaka a sirrance da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati na Shugaban Kasa, Bola Tinubu, Hon. Femi Gbajabiamila da gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, domin ya samu wa’adi na biyu a matsayin gwamnan Delta.
Shugabannin jam’iyyar PDP na Jihar Delta, sun tofa albarkacin bakinsu game da soyayyar Oborebwori da shugabannin APC. Shugabannin jam’iyyar, wato Mista Theophilus Ekiyor, Mista Ochuko Oghenekome, da Mista Ezekiel Chukwudi, a wata budaddiyar wasika, sun zargi gwamnan da yin akala a sirrance da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila da gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, domin ya samu na wa’adi na biyu a matsayin gwamnan Delta.
Idan za a iya tunawa dai, dan majalisar tarayya kuma diyar tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu, ta fice daga PDP zuwa APC a bara. Ibori dai ya yi zamani da Tinubu a matsayin gwamna a 1999 kuma makusancinsa ne.
Sai dai gwamnonin sun musanta wannan jita-jita, inda suka yi magana ta bakin mukarrabansu cewa ba za su bar jam’iyyarsu zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba.
Haka zalika jam’iyyunsu sun bayyana irin wadannan ikirari a matsayin yaudarar jam’iyya mai mulki, inda suke neman haifar da rudani a cikin jam’iyyunsu da kuma zargin gwamnonin.