Yanayin farashin Man Fetur a daukacin nahiyar Afrika a 2025, ya kara habaka saboda samar da yanayin makamashi, duba da ya yadda ake kara samar da shi da kuma yawan wanda ake fitarwa zuwa ketare.
A kasashe kamar su Libiya da Angola da ke da dimbin Man da suke adane da shi, na ci gaba da sayar da shi kan farasshi mai sauki, inda kasashe kamarsu, Ethiopiya da Liberiya, suka dogara da shigo da man daga ketare, ke fuskantar tsadar farashinsa.
- Bajintar Aiki: Majalisar Dattawa Ta Jinjina Wa Ministan YaÉ—a Labarai
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
Duba da tashin farashinsa a kasuwar duniya, hakan ya sanya da fuskatar kalubale kamar na samar da tallafi da samar da shi, musamman domin su sayarwa da alumarsu, kan farashi mai sauki.
A cewar kafar sanar da farashin man ta duniya wato GlobalPetrolPrices.com, ta jere sunayen kasashe 10 da za su sayar da Man a farashi mai sauki, a 2025.
1 Libiya: Ta ci gaba da zama jagora a tsakanin kasashen da ke Afirka wajen sayar da Man da sauki, inda Litarsa daya, ake sayarwa kan dala 0.030. Hakana ya kasance ne, saboda ta na da dimbin Man mai yawa
2 Angola: Ana sayar da Man Lita daya kan dala 0.328, duba da cewa, kasar ta kasance kan gaba wajen samar da man a Afirka kuma tana da shiyar mai yawa wajen sayar da man, a kasuwar duniya.
Fitar da shi mai yawa da ke yi zuwa kasashen waje, hakan ya sanaya tana sayarwa da ‘yan kasar, kan farashi mai sauki.
3 Masar: Ana sayar da Lita daya, kan dala 0.336, duba da cewa, kasar na da dimbin zuba hannun jari a fannin Mai da Iskar Gas a shekaru da dama, kuma kasar na samar da tallafi a Mai.
4 Algeriya: Ana sayar da Lita daya kan dala 0.339, kuma kasar na da wadatar mai da albarkatun Iskar Gas, wanda hakan ya sanya, ta ke sayar da Man kan farashi mai sauki.
5 Sudan: Ana sayar da Lita daya kan dala 0.700, wanda har yanzu, wannan farashin yake kasa da yadda ake sayarwa, a kasuwar duniya.
6 Nigeryia: Ta kasance kan gaba wajen samar da Mai a Afirka, tana sayar da Lita daya, kan dala 0.769. Duba da yadda ta kasance kan gaba a najiyar wajen fitar da shi, amma saboda tsare-tsaren Gwamnatin kasar hakan ya sanya farashinsa, na sauya a duniya.
Farashinsa, ya kasance a dan kasa kadan da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, wanda kuma ake kalubalen da .
7 Tunisiya: Ana sayar da Lita daya kan dala 0.794, kasar ta kasance ta na da karancin Man da take samarwa, amma ta fi samun kudin shiga daga Man da take sayarwa a kasuwar yankuna kuma Gwamnatin kasar, na samar da tallafi ga Man, domin ta kare farashinsa
8 Ethiofiya: Kasar ce ta takwas a cikin wannan jeren, inda ake sayar da Lita daya kan dala 0.805. Sai dai, kasar ta kasance ba ta a cikin manyan kasashen da ke samar da Man, domin akasari, tana shigo da Man ne, amma bisa kokarin Gwamnatin kasar, tana daidaita farashinsa, domin sayarwa da ‘yan kasar kan farashi mai sauki.
9 Liberiya: Kasar ta dogara ne, wajen shigo da Man domin ta cimma bukatar shi, ta cikin gida, inda kuma ake sayar da Lita daya kan dala 0.829
10 Gabon: Ta kasance tana daga cikin kasashen da ke Man mai yawa, inda ake sayar da Lita daya kan dala 0.944, wanda hakan ya nuna cewa, farashinsa da sauki idan aka kwatanta da sauran kasashen da ke a nahiyar.