Mako daya gabanin kafuwar sabuwar gwamnatin Amurka, kafofin yada labarai na sassan kasa da kasa sun fara yin kira ga kasashen Sin da Amurka, da su yi hadin gwiwa don tinkarar kalubalolin duniya tare. Kiran da al’ummun duniya ke yi na alamanta fatan cewa, wadannan manyan kasashe biyu za su iya zama karfi mafi muhimmanci wajen wanzar da zaman lafiya, da karko, da ciyar da bunkasuwar duniya baki daya gaba.
A yau shekaru 80 da suka gabata, Sin da Amurka sun gudanar da hadin kai da sauran kasashe masu kaunar zaman lafiya, sun yi gwagwarmaya tare don cimma nasarar yakin kin tafarkin murdiya. A halin yanzu kuma, rikicin Ukraine, da tashin hankali tsakanin Palasidinu da Isra’ila, na haifarwa sauran wurare mumunan tasiri, wanda ya sa ake fuskantar kalubale mai tsanani a bangaren zaman lafiya da tsaro.
- Me Ya Sa “TikTok Refugee” Na Amurka Suke Ta Kama REDnote Ta Kasar Sin
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 7 Cikin Jerin Sassan Da Ba Za A Iya Dogaro Da Su Ba
Dole ne Sin da Amurka su sauke nauyin dake wuyansu, a matsayinsu na manyan kasashe masu karfi, wato dai su yi mu’ammala da juna yadda ya kamata, da kauracewa kawowa juna cikas.
Shin ko ta yaya za su iya yin mu’ammala mai kyau? Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da shawarwari masu ma’ana guda 7, yayin da yake ganawa da takwaransa na Amurka a watan Nuwamban bara a birnin Lima. Matakin da ya baiwa bunkasuwar huldar dake tsakanin kasashen biyu mafita mai kyau a nan gaba, kuma ya karawa kasashen biyu kwarin gwiwa wajen sauke nauyin dake wuyansu tare.
Ya ce ya kamata a sauke nauyi bisa karfin kai. Kamar yadda Sin da Amurka suke yi a yau shekaru 80 da suka gabata. A halin yanzu, dole ne kasashen biyu su sauke nauyin da ya wajaba a kansu na tarihi, da al’umma da duniya, duba da cewa ana fuskantar sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba, ya kamata su kara hadin gwiwarsu, da gaggauta taimakawa saura, don ba da tabbaci, da ingantaccin karfi mai yakini, ga duniya dake fama da tashe-tashen hankula. (Amina Xu)