Da sanyin safiyar yau Alhamis, an garzaya da shahararren jarumin fina-finan Bollywood, Saif Ali Khan, asibiti a birnin Mumbai bayan wani mutum da ba a san ko wane ne ba ya daɓa masa wuƙa a gidansa.
Rahotanni sun bayyana cewa jarumin ya samu raunuka har guda shida sakamakon wannan harin.
BBC Hausa ta ruwaito cewa, kafin aukuwar lamarin, Khan ya yi cacar baki da mutumin wanda daga bisani ya kutsa cikin gidansa da tsakar dare, kamar yadda Mataimakin Kwamishinan ‘Yansandan Mumbai, Dixit Gedam, ya tabbatar wa manema labarai.
An yi wa jarumin tiyata kuma yana samun sauƙi a halin yanzu, kamar yadda masu taimaka masa suka bayyana.
Wannan al’amari ya janyo cece-kuce a tsakanin masoya da mabiyansa a duniya.