Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da jajircewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake yi na kammala aikin titin Abuja zuwa Kano cikin wata 14.
Da yake magana yayin wata ziyara ta duba aikin a garin Tafa, Jihar Neja, a ranar Alhamis, Idris ya bayyana cewa jajircewar Shugaban Ƙasa wajen hanzarta aikin ya sa aka bai wa wani kamfani kwangilar wasu sassan aikin da aka fara bai wa kamfanin Julius Berger PLC.
- Ba Zan Ci Gaba Da Zama A Liverpool Ba -Salah
- An Gudanar Da Somin-Tabin Shirye-Shiryen Murnar Bikin Bazara Na CMG A New York
Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya himmatu matuƙa wajen ganin an kammala aikin titin Abuja zuwa Kano da ta ratsa Kaduna da Zariya, kuma ya dage cewa dole a kammala wannan aiki. Ba za mu bari wani ɗan kwangila ya tilasta wa gwamnati ta bi sharuɗɗanshi kan wannan aiki ko wani aiki ba. Ba mu da isasshen lokaci na jira na tsawon wasu shekaru uku kafin a kammala wannan titi.
“Ministan Ayyuka ya bayyana cewa sun sanya wa kan su wa’adin watanni 14 don kammala wannan titi.
“Ganin irin ƙwazo da jajircewar da suke nunawa, mun yi imani za a cika wannan wa’adi.
“Ga waɗanda suke siyasantar da wannan aikin titi, don Allah ku ajiye siyasa a gefe. Wannan titi dole ne a kammala shi. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya himmatu matuƙa wajen ganin wannan babbar hanyar da ke haɗa Abuja da Kano da sauran jihohi an kammala ta. Babu abin da zai hana hakan.”
Idris ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya ƙi amincewa da wa’adin shekaru uku da kamfanin Julius Berger ya bayar, inda ya ba da umarnin kammala aikin a cikin gaggawa.
An raba aikin zuwa kashi uku domin sauƙaƙa gudanarwa da tabbatar da cewa an kammala shi cikin lokaci.
Idris, wanda ya samu rakiyar Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, da wasu manyan jami’ai, ya yaba wa jajircewar Umahi, inda ya jinjina masa kan ƙoƙarin sa wajen rage kuɗin kwangilar da kuma wa’adin kammalawa.
Ya bayyana cewa da farko Julius Berger sun nemi ƙarin kuɗin kwangilar daga Naira biliyan 797 zuwa Naira tiriliyan 1.5 tare da ƙarin wa’adi zuwa shekaru uku.
Sanata Umahi ya bayyana cewa ma’aikatar ta samu amincewa daga Hukumar Kula da Sayen Kayayyaki ta Ƙasa (BPP) kan sabon kuɗin kwangilar Naira biliyan 252.89, wanda za a gabatar wa Majalisar Zartaswa ta Tarayya domin amincewa.
Sabon tsarin ya haɗa da ƙarin wasu kilomita a ɓangaren Kano, sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana, da kuma tanadi don kula da titin a nan gaba.
Idris ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su daina siyasantar da aikin, su mayar da hankali kan ganin an kammala shi, yana mai jaddada muhimmancin sa wajen haɗa Babban Birnin Tarayya da Kano da sauran jihohin arewa.