Akalla ‘yan bindiga 7 ne aka kashe, sannan aka kwato shanu 109 da aka sace a wani farmaki da rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta gudanar a cikin nasara, biyo bayan wani harin da aka kai kauyen Ruwan Doruwa da ke karamar hukumar Dutsinma a jihar.
Kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar, ta ce an kai samamen ne a ranar Asabar, 18 ga watan Janairu, 2025, da misalin karfe 9:00 na safe.
- Zargin Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Bankawa Keken Adaidaita Sahu Wuta A Kano
- Ƴansanda A Gombe Sun Yi Holar Masu Laifuka
DSP Sadiq ya ce, hedikwatar ‘yansanda ta Dutsinma ta samu kiran gaggawa kan rahoton cewa, ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 da wasu muggan makamai, inda suka kai farmaki kauyen Ruwan Doruwa.
Nan take, jami’in ‘yansanda, DPO tare da hadin gwiwar sojoji, DSS, da masu sanya ido kan tsaro na cikin al’umma (KTSCWC) na jihar Katsina, da ’yan banga suka farmaki ‘yan bindigar.
Jami’an tsaron sun yi artabu da ‘yan bindigar, inda suka kashe bakwai daga cikinsu sannan sauran suka gudu da raunuka.
Wadanda aka ceto yayin artabu da ‘yan bindigar sun hada da shanu 61, tumaki 44, jakuna biyu, akuya daya, da kare daya.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yabawa ‘yansandan bisa jajircewarsu da kwarewa.