Hukumar UNICEF ta ce tana buƙatar sama da dala miliyan 250 don magance matsalolin da suka addabi yara ƙanana a Jihohin Sakkwato, Zamfara, da Katsina.
Daga cikin adadin, jihohin uku za su ci daga dala miliyan 100 domin samar da abinci mai gina jiki, kiwon lafiya, da ilimi ga yara.
- Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
- Sabon Albishir Ga Masu Kawo Ziyara Ko Yada Zango A Birnin Beijing Na Kasar Sin
Da ta ke magana a taron manema labarai a Gusau, wakiliyar UNICEF, Ms. Cristian Munduate, ta bayyana cewa a Zamfara kawai, yara 400,000 ‘yan Æ™asa da shekaru biyar suna fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Sannan yara sama da 200,000 a yankin Arewa Maso Yamma ke buƙatar shirye-shiryen Abinci Mai Gina Jiki (RUTF) a 2025.
Haka kuma, yara sama da 300,000 a jihohin Sakkwato da Zamfara ke buƙatar rigakafin cutar ƙyanda, sannan mutane miliyan biyu a jihohin biyu suna buƙatar magani da shawarwari kan abinci mai gina jiki.
Ms. Cristian ta yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su:
- FaÉ—aÉ—a ayyukan kiwon lafiya da Æ™arfafa shirye-shiryen kiwon lafiyar al’umma.
- Samar da abinci mai gina jiki ga yara masu rauni.
- Haɓaka ilimi da kayan makaranta.
- Samar da rigakafin yau da kullun don kare yara daga cututtukan da za a iya hana su.
Ta ce É—aukar matakin gaggawa yana da muhimmanci don ceto rayuka da gina kyakkyawar makoma ga yara a Zamfara, Sakkwato, Katsina, da sauran yankunan Nijeriya.