Sakatare-janar na kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping ya shiga cikin sanyi ya ziyarci mutanen da ambaliyar ruwa ta daidaita a wani kauyen dake birnin Huludao na lardin Liaoning da birnin Shenyang, hedkwatar lardin dake arewa maso gabashin kasar, a jiya Laraba da kuma a yau Alhamis.
A jiya Laraba, shugaba Xi ya ziyarci kauyen Zhujiagou, dake birnin Huludao, wato daya daga cikin biranen da ambaliyar ruwa na lokacin zafi ta fi shafa a shekarar 2024.
- UNICEF Ta Nemi Dala Miliyan 250 Don Tallafa Wa Yara A Sakkwato, Zamfara Da Katsina
- Farashin Man Fetur Ya Ƙaru A Abuja Da Legas
A kauyen, Xi ya duba irin ci gaban da aka samu wajen farfado da kuma sake gina yankin bayan bala’in.
Da yake ziyartar mazauna kauyukan da suka koma cikin sabbin gidajensu kafin wannan lokacin sanyi, Xi ya yi tambaya game da ingancin gidajen da aka sake ginawa, da kuma ko sun gamsu da yanayin rayuwarsu na yau da kullun.
Sannan a yau Alhamis, Xi Jinping ya kai ziyara birnin Shenyang, domin ganewa da idonsa kan yadda mazauna birnin suke murnar Bikin Bazara na bana.
Bikin Bazara yana zaman biki mafi muhimmanci ga al’ummar Sinawa, wanda a bana ya fado a ranar 29 ga watan nan na Janairu. ( Mohammed Yahaya, Fa’iza Mustapha)