Sakewa gabar tekun Mexico suna, sake mallakar yankin ruwa na Panama, sayen yankin Greenland…
Wani nazarin jin ra’ayin jama’a da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar a kan intanet, ya nuna yadda kaso 78.6 na wadanda suka bayar da amsa suka yi kakkausar suka kan niyyar sabuwar gwamnatin Amurka na fadada yankunan kasar, suna kiran hakan da cin zali da babakere da danniya.
- Sojoji Sun Kai Farmaki, Sun Kashe Ƴan Ta’adda Masu Yawa A Neja
- Ƙasashe 7 Sun Mara Wa Nijeriya Baya Don Kafa Cibiyar Koyar Da Ilimin Yaɗa Labarai Ta UNESCO – Minista
Cikin nazarin, kaso 72.3 na wadanda suka bayar da amsa sun yi imanin cewa, shirin Amurka na fadada yankunanta na da nufin kare muradun kasar na yi wa duniya babakere. Wani mai amfani da intanet ya wallafa cewa “ya kamata a nuna turjiya ga ra’ayin babakere, ba tare da la’akari da duk wata hujja ko bayani da Uncle Sam(Amurka) zai yi amfani da shi ba.
Mutane 7083 ne suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24, ga nazarin wanda kafar CGTN ta wallafa cikin harsunan Ingilishi da Faransanci da Larabci da kuma Rashanci. (Fa’iza Mustapha)