A jiya ne, kasar Sin ta fitar da takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da dinkuwar kasar Sin a sabon zamani”, inda aka bayyana cewa, kamata ya yi a bar jama’ar kasar Sin su yanke shawara kan al’amuran kasarsu.
Wannan na nufin, batun Taiwan, harkokin gidan kasar Sin ne, wanda ya shafi babbar moriyar kasar, da kaunar da Sinawa suke nuna wa kasarsu, don haka ba su yarda da tsoma baki daga kasashen ketare ba.
Kafin fitar da takardar bayanin, shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Pelosi, ta ziyarci yankin Taiwan na kasar Sin, ba tare da amincewar gwamnatin Sin ba, batun da ya lalata yanayin tsaron zirin Taiwan, da tsananta rikici tsakanin Amurka da Sin.
Dangane da wannan batu, kasar Sin ta fitar da wannan takardar bayani, don mayar da martani ga ziyarar da Pelosi ta kai yankin Taiwan, tare da yin cikakken bayani kan dabarun kasar Sin dangane da yadda za a daidaita batun Taiwan a sabon zamani, ta yadda hakan zai taimaka a kokarin tabbatar da zaman lafiya da walwala a yankin Asiya da tekun Pesific, gami da sauran wurare a duniya baki daya.
A karon farko, takardar bisa tsari ta bayyana fatan sake hadewar bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan cikin lumana, a karkashin tsarin “kasa daya, tsarin mulki iri biyu”. Wanda ya nuna irin babban ci gaban da yankin Taiwan zai iya samu, da ba da tabbaci ga moriyar mutanen yankin Taiwan, da samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki a yankin Asiya da tekun Pasific, da ma sauran sassan duniya, da makamantansu.
A karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, jama’ar kasar da yawansu ya kai fiye da biliyan 1.4 suna son ganin dinkuwar kasarsu cikin lumana, sai dai ba za su taba hakura da yunkurin ‘yan aware na neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin ba.
Sinawa suna da niyya mai karfi ta fuskar kare mulkin kai da cikakkun yankunan kasarsu, kana suna da hikima, da jajircewa da ake bukata, wajen tabbatar da dinkuwar kasar Sin a nan gaba. (Bello Wang)