Nan ba da jimawa ba, masu sana’ar POS za su kara kudin caji a dukkanin Fadin Nijeriya, biyo bayan amincewa da karin kashi 50 cikin 100 da gwamnatin tarayya ta amince ga kamfanonin sadarwa.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar masu sanar ta POS da na bankunan Nijeriya (AMMBAN), Ogungbayi Ganiyu; shi ne ya sanar da hakan, inda ya yi nuni da irin tasirin da karin kudin zai yi ga kasuwansu.
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
- Dole Mu Bai Wa Matasan Nijeriya Dama A 2027 – Bafarawa
Ganiyu, ya jaddada cewa, masu wannan sana’a; sun raja’a ne kacokan kan kamfanonin sadarwa, musamman ta hanyar amfani da data, domin aiwatar da kasuwancinsu.
“Ko shakka babu, wannan kari zai yi matukar tasiri ga mambobinmu. Sannan, ina jin tsoron hakan na iya yin tasiri kwarai da gaske, wajen karin yawan kudaden caji ga kwastomomi”, in ji Ganiyu.
Har ila yau, ya ambaci cewa, duk da yunkurin da masu gudanar da sana’ar ta POS ka iya yi; na kin kara kudin cajin ga, amma sai dole ta sa su yin karin; saboda matsin lamba da kuma kokarin ci gaba da aiwatar da kasuwancinsu.
“Duk da cewa, ba mu zauna mun duba sabon tsarin karin ba a cewarsa, amma dai tattaunawa za ta bayar da hasken matakan da suka kamata a dauka nan gaba”.
LEADERSHIP, ta rawaito cewa, tuni kungiyar masu sana’ar ta hanyar kafofin sadarwa na kasa (NATCOMS), ta sha alwashin kalubalantar gwamnatin tarayya a gaban kotu, kan wannan karin haraji na kashi 50 cikin 100.