Kakakin Majalisar Wakilai, Rt Hon Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa an gabatar da ƙudirori har sama da 15 da suka shafi samar da abinci don magance yunwa, waɗanda ke matakai daban-daban na aiwatarwa.
Daga cikin su akwai dokar kafa hukumar tanadin abinci ta ƙasa da dokar kafa cibiyar sarrafa abinci a Kwara. Ya bayyana hakan a taron Daily Trust na 22 wanda ya mayar da hankali kan tsaron abinci. Abbas ya ce majalisar tana aiki wajen samar da tsare-tsaren da za su tallafa wa manoma da tallafi hanyoyin noma noma na zamani.
- Za Mu Dawo Da Martabar Gidajen Sinima A Arewa – Ali Nuhu
- Rikicin Ƙabilanci Da Saɓanin Makiyaya Da Manoma Ya Zama Tarihi A Jihar Kaduna – KSPC
Haka zalika, Abbas ya bayyana cewa rashin tsaro yana taka muhimmiyar rawa wajen haifar da ƙarancin abinci. Ya ce gwamnati na ƙoƙarin dawo da manoma gonakinsu don ƙaruwar samar da abinci.
A cewarsa, rahoton Cadre Harmonise na 2024 ya nuna cewa ‘yan Nijeriya miliyan 31.8 suna fama da matsalar ƙarancin abinci. Haka kuma, ya ce an ware kudi a kasafin kudin 2025 don fannin noma, da nufin magance matsalolin wadatar abinci.
A nasa ɓangaren, Ministan ci gaban dabbobi, Idi Maiha, ya ce burin kawar da yunwa wajibi ne da ke buƙatar haɗin kan gwamnati da masu zaman kansu. Ya ce Nijeriya na fuskantar ƙarancin abinci saboda mafiya yawan hanyoyin da manoma ke amfani da su marasa ɗorewa ne da rashin kula da albarkatun ƙasa. Ya bukaci ɗaukar matakai masu ɗorewa don tabbatar da abinci mai yawa da arha ga kowa.