Tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, zai ayyana sha’awar tsayawa takarar kujerar sanatan Filato ta tsakiya a jam’iyyar Labour Party (LP).
A ranar Litinin ne aka sako Dariye da tsohon gwamnan Taraba, Jolly Nyame, da wasu mutane uku daga gidan yari, watanni uku bayan afuwar da majalisar jihohi karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi musu a ranar 14 ga Afrilu, 2022.
Dariye, wanda aka yanke wa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1.126, an masa afuwa bayan shafe kimanin shekaru hudu a gidan yarin.
Daily trust ta rahoto cewa, ta ji daga majiya mai tushe cewa Jam’iyyar LP reshen jihar Filato ta kammala shirye-shiryen karbar tsohon gwamnan Filato daga Abuja domin karbar fom din takarar sanata a jam’iyyar.
Dariye wanda ya taba zama gwamnan jam’iyyar PDP amma daga baya ya fice daga jam’iyyar. Ya yi takara kuma ya lashe kujerar Sanata a 2011 a Jam’iyyar LP.
Wani jigo a jam’iyyar LP, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce: “Eh, gaskiya ne shi (Dariye) zai tsaya takarar kujerar Sanata. Muna shirye-shiryen zuwan shi daga Abuja domin ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Sanata”.