Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce hannuwan ‘yan siyasar Amurka, da “‘yan ina da yaki”, na jike da jinin al’ummun gabas ta tsakiya.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, ya ce rahoton bincike da aka yi mai taken “Matukar keta hakkokin bil adama da Amurka ta aikata a gabas ta tsakiya da sauran wasu sassan duniya”, wanda kuma kungiya mai nazarin harkokin da suka jibanci kare hakkin bil adama ta Sin ta wallafa, ya nuna yadda Amurka ta keta hurumin bil adama a gabas ta tsakiya, da sauran yankunan dake kewayen yankin ta fannoni 3.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, duba da yadda hannuwan ‘yan siyasar Amurka, da ‘yan ina da yaki, ke jike da jinin al’ummun gabas ta tsakiya, bai kamata a ce irin wadannan sassa suna da ta cewa, a fannin kare hakkokin bil adama, ko su zamo masu yanke hukunci a fannin ba.
Daga nan sai ya yi kira ga karin al’ummun gabas ta tsakiya, da su tashi tsaye, wajen nuna adawa da danniya, da cin zalin da Amurka ke yi musu.
Kaza lika ya yi kira ga kwamitin kare hakkokin bil adama na MDD, da ofishin babban kwamishinan MDD mai lura da batun kare hakkin bil adama, da su kara sanya ido kan laifukan da Amurka ta aikata a gabas ta tsakiya, da ma sauran wasu yankunan duniya, tare da daukar matakan da suka dace. (Saminu Alhassan)