Yau Litinin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta mayar da martani ga sanarwar hukumar leken asiri ta Amurka wato CIA, inda ta jaddada cewa, kamata ya yi bangaren Amurka ya daina siyasantar da batun gano inda cutar numfashi ta COVID-19 ta bulla.
Hukumar CIA ta ce, ta yi imani da yiwuwar bullar cutar daga dakin gwaje-gwaje maimakon yaduwa daga dabbobi.
- Bikin Bazara Na Kasar Sin Na Samun Karbuwa Daga Masu Yawon Shakatawa Na Duniya
- Shugaba Xi Ya Yaba Da Ci Gaban Kasar Sin Duk Da Kalubalen Da Aka Fuskanta A Shekarar Dragon
A martaninta ga wannan lamarin, Mao Ning ta yi nuni da cewa, bai yiwuwa a ce aka samu bullar cutar daga dakin gwaje-gwaje ba, kuma wannan hujja ce ta kimiyya da kungiyar kwararru ta hadin gwiwar Sin da WHO ta tabbatar bisa ziyarar da ta kai dakunan gwaje-gwaje da batun ya shafa a Wuhan, da zurfafa mu’amala da masu bincike na kimiyya masu ruwa da tsaki, wanda al’ummar duniya da masana kimiyya suka amince da su sosai.
Mao Ning ta kara da cewa, kamata ya yi Amurka ta daina zargi da bata wa wasu kasashe suna, ta mayar da martani game da halaltattun damuwar kasashen duniya da wurwuri, da daukar matakin mika bayanai game da rahotannin farko na bullar cutar ga hukumar ta WHO, da yin karin bayani don kawar da shakku kan dakunan gwaje-gwaje na nazarin halittu na Amurka, da ba da bayanai bisa sanin ya kamata ga mutanen duniya. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp