Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci.
Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne.
- Tinubu Ga Peter Obi: Ka Gargaɗi Magoya Bayanka Kan Ɓata Min Suna
- Kasar Sin Ta Bukaci A Tallafa Wa Kasashen Afirka Don Inganta Karfinsu
Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba.
Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ge ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha da ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna.
Idan kayan yaki ne ma a ajiye su nukiliya, da manyan tankokin yaki da su jiragen yaki sai dai a yi amfani da su kwari da baka da takubba, idan an tari abokan gaba da wadannan an yi bidi’a kamar yadda fahimtar wadancan mutanen take. Ka ga idan aka yi haka ai hankali ya warware.
Kur’anin da Allah ya saukar mana zamaninsa ba ya shudewa, ya dace da kowane irin zamani da ya zo, ko zai zo a nan gaba.
Ayoyin da suka sauka suna nan suna mana hukunci, ba a kula da ko dan waye suka sauka, ko don me suka sauka, abin ya zama hukunci ga al’ummar Annabi duka tun daga wancan zamanin da aka saukar har zuwa tashin kiyama.
Misali ayar da ta ce, “ku sani, hakika Annabi yana cikinku”, wasu sai su ce da su Sayyidina Abubakar ake, ban da mu a zamanin nan. Alhali kuwa ba haka ba ne, duka Malamai na Allah sun fassara wannan da cewa Annabi (SAW) yana nan a cikin al’ummarsa har zuwa tashin kiyama.
Idan kuwa masu wancan fahimtar suka dage sam sai an tsame Annabi ba ya tare da da al’ummarsa, sai mu ce, ke nan ayar da ta umurce mu mu kadaita Allah “ku yi sani babu abin bautawa da gaskiya sai Allah” da Sahabbai kawai ake yi.
Kun ga ai babu wanda zai karbi wannan. To, haka shari’ar Manzon Allah take, ta dace da duk irin sauyin da za a samu na zamani.
Akwai hadisai da yawa da Annabi (SAW) yake so ya ga al’ummarsa tana cikin nishadi ba cikin kunci ba. Manzon Allah yana so ya ga Musulmi ya fita daban da saura kamar kitse a cikin nama, ya yi ado ya yi kyau.
Don haka, za mu yi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, ba bidi’a ba ne, sunnah ce ta Manzon Allah, sunnah ce ta Khalifofinsa, Musulmi su yi murna su yi nishadi. Addini ba ya zo ne ya tattakure mutane ya hana su sakat ba, har ma a samu wasu suna barin addini zuwa wasu saboda takura, a uzu billahi.
Irin haka ta faru a Ibadan, wasu Musulmi sun kawo kara wurin Shehu Ibrahim cewa matasansu suna zuwa coci saboda kidar da ake yi a can, Shehu ya ce musu to ku wa ya hana ku kidar? Ka ga dole (masu irin waccan fahimtar) su shiga karatu sosai a nan wurin (kafin su kai ga cewa kaza ya haramta, kaza ya halasta).
Saboda haka a bar mutane su yi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, Sarkin Musulmi ya sanar, Malamai su yi bayani, al’ummar musulmi su taya juna murna, Alhamdu lillah.
Kamar yadda muka fada, yana daga cikin abin da ya sa Sahabbai ba su sanya farkon shekarar Musulunci a Rabi’ul Auwal ba don kar a hade manyan bukukuwanmu biyu a wuri daya, ga bikin haihuwar Annabi (SAW) ga kuma na shiga sabuwar shekara, kamar dai yadda Sayyidina Aliyu (Karramallahu wajhahu) ya hana a yi ramakon Ramadan a cikin goman farko na watan Zulhajji, don kar wani ya kwace wani, alhali kowannensu yana da girmansa da falalarsa.
Don haka, a bar Mauludin Manzon Allah da girmansa da falalarsa, shi ma shiga sabuwar shekarar Musulunci a barshi da nashi.
Sannan me ya sa Sahabbai ba su kafa shekarar ta Musulunci da ranar da aka aiko Manzon Allah da Manzanci ba, sai dai Hijira?.
Haka nan me ya sa ba su kafa da ranar da aka kammala saukar da Shari’ar Manzon Allah (SAW) ba, ko ranar Fatahu Makkata (ranar da aka bude Makka)? Sahabbai duk sun san da girma da falalar wadannan ranakun, amma duk idan aka hadasu, daya zai kwace wa daya.
Alheran da ke cikin falalar Hijira suna da yawa. Daga ciki shi ne ‘yan’uwatanka da Manzon Allah ya hada a tsakanin Muhajirai da Ansaru, mutanen Makka da masu masaukinsu na Madina. Haka nan da ‘yan’uwantaka a tsakanin su kansu Muhajiran, kamar yadda ya hada a tsakanin Sayyidina Hamza (RA), wanda yake Baffansa, Balarabe, Bakuraishe da kuma bawansa mai masa hidima Zaidu bin Harisata.
Kuma saboda wannan ‘yan’uwantakar, Zaidu ya shiga cikin su Sayyidina Aliyu da wansa Ja’afaru bin Abiy dalibi wajen neman a bashi rainon ‘yar Sayyidina Hamza wadda Manzon Allah ya taho da ita daga Makka lokacin da ya je ramuwar Umura.
Da aka tambaye shi me ya sa yake so a bashi rainonta, Zaidu ya ce saboda ‘yar dan’uwana ce. To daga baya dai Manzon Allah ya bai wa Ja’afar ita saboda bayan kasancewarta ‘yar Baffansa yana kuma aure da ‘yar’uwar mahaifiyarta.
To, ka ga girman ‘yan’uwantaka ta Musulunci. Irin wannan ma ana gani kuru-kuru a tsakanin wadanda suka sha Faila, ‘yan’uwa su shaku da juna su zama uwa daya uba daya.
Haka shauran Musulmi ma duk a yi kokari a zama haka. ‘Yan’uwantaka in ta faru, komai ya faru, idan soyayya ta samu komai ya samu.
Kafin Hijira, Manzon Allah (SAW) ya koya mana yadda za mu yi addini idan ka tsinci kanka a cikin wadanda ba musulmi ba kuma ba su yarda da Musulunci ba, kamar yadda ya rika yin sallah a Ka’aba duk kuwa da kasancewar daruruwan gumaka a ciki.
Yana sallah yana kallon Ka’aba kuma da gumaka a ciki sannan bai ce zai cire ko daya ba, shi dai ya san Allah yake wa sallah ba gumaka ba.
Haka nan ya koyar da yadda za a yi addini a wurin mutanen da za su barka ka yi addininka, amma ba su so ka kawo musu naka ka bata musu tsarinsu, kamar yadda Sahabbai suka yi a Habasha. Saboda kyawawan halayensu da wasu ‘yan garin suka gani suka musulunta bisa radin kansu.
Don haka kar mutum ya yi ta fada ya ce dole sai ya sauya wa mutanen da yake cikinsu tsarinsu da suka yarda da shi.
Manzon Allah ya nuna mana zama a kasar da Musulmi sun fi yawa amma kuma akwai wadanda ba musulmi ba a ciki, kamar zaman Madina.
Ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da wadanda ba musulmin ba. A kare wa duk ‘yan kasa hakki bisa tsarin zamantakewarsu, duk abin da zai amfani kasa na kowa ne, haka nan duk abin da zai cuci kasa ya shafi kowa za a fito a yi taron dangi a kai.
Haka aka zauna har sai da Yahudawa suka ha’inci Manzon Allah (SAW) ya kore wasu daga Madina wasu kuma aka kashesu.
Kuma duk da wannan, Manzon Allah (SAW) saboda shi Annabin Rahama ne ya ba Yahudawan dama su zabi alkalin da zai musu hukuncin abin da suka yi, suka zabi Sa’adu bin Mu’azu. Hukuncin da ya yanke kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ya yi dai-dai da hukuncin da Allah ya yanke.
Don haka, ko da wani zai ce ai Manzon Allah ya yanka Yahudawan Banu kuraiza don ya samu kafar ta da rikici a kasa, sai a ce masa ba haka abin yake ba. Su Banu kuraiza hukuncin da ya dace da su kenan a ka’idar duniya.
Duk wanda ya ha’inci kasarsa ya hada kai da abokan gaba ana yaki hukuncin kisa ya hau kansa. Kuma ko waye ba Musulmi ba kawai irin hukuncin da zai yi kenan.
Haka aka kori Banud Nadir da Banu kainu ka’a, Madina ta zama kasar Musulunci, Manzon Allah (SAW) shi ne shugaba mai shari’a da littafin Allah Alkur’ani. Duk dai abin da za mu koya mu yi aiki da shi ne zaman Manzon Allah a Makka, zaman Sahabbansa a Habasha da kuma zamansa a Madina (SAW).
Wannan yana daga cikin albarkar Hijira.