Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al-Hilal da ɗan wasan Brazil Neymar sun amince su kawo ƙarshen kwantaraginsu.
Neymar, ɗan shekara 32, ya koma Al-Hilal ne a watan Agustan 2023 kan kuɗi Yuro miliyan 90.
- Firaministan Sin Ya Tattauna Da Baki Kwararru Dake Kasar
- An Watsa Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na CMG A Karon Farko A Najeriya
Sai dai rauni ya hana shi buga wasa, inda ya yi wasa bakwai kawai tun lokacin da ya koma ƙungiyar.
A kakar da ake ciki, Neymar ya buga wasa sau biyu kacal, kuma na ƙarshe shi ne lokacin da aka yi canji da shi a watan Nuwamba.
Ana hasashen Neymar zai koma ƙungiyarsa ta gida, Santos, da ke Brazil.
“Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar.
Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar.
A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara.
Lokacin da ya koma ƙungiyar, Neymar ya bayyana burinsa na kafa tarihi, amma raunin da ya samu yayin wasan Brazil da Uruguay a shekarar 2023 ya hana shi buga wasanni da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp