Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da dage bikin kamun kifi karo na 61 daga watan nan na Fabrairu, zuwa shekarar 2026. Dagewar bikin ya biyo bayan zaman tattaunawar da aka gudanar tsakanin Majalisar masarautar Argungu da kuma gwamnatin jihar.
“An yanke shawarar dage gudanar da bikin ne, don ya zama wajibi da buƙatar aiwatar da wasu abubuwa da yin wasu tanade-tanade.”
- Ba Za Mu Bari A Yi Wa Olmo Rajista A Barcelona Ba – Javier Tebas
- Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi
Sanata Umar Tafawa ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema Labarai da ya gudanar a ofishinsa da ke Birnin Kebbl.
Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu.
“Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.