Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta sake jaddada cewa za ta fara aiwatar da dokar tilasta yin insuran motoci na daga ranar 1 ga Fabrairu, 2025, bisa umarnin babban Sufeto Janar na ‘Yansandan Nijeriya, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin inganta tsaro a kan tituna da tabbatar da cewa duk masu motocin suna da inshorar da ta dace don kare kansu da sauran masu amfani da tituna.
- EFCC, ICPC Sun Kwato Naira Biliyan 277.69 Da Dala Miliyan 106 A Shekara Guda
- Yadda Turmutsutsin Rabon Kayan Abinci Ya Dagula Karsashin Kirsimeti
Rundunar ta gargaɗi masu motoci da direbobi kan ƙin bin wannan doka, inda ta bayyana cewa duk wanda ba shi da inshorar zai fuskanci hukunci daidai da dokokin da suka dace, wanda zai iya haɗa wa da tara, da horo ko duka biyun.
Sufeto Janar na Ƴansandan ya umarci kwamishinonin Ƴansanda na jihohi da su tabbatar da aiwatar da wannan doka, inda jami’an Ƴansanda za su riƙa binciken inshorar motoci tare da aiwatar da hukunci ga masu karya doka.
Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta jaddada ƙudirorinta na tabbatar da tsaro a kan tituna da kare rayukan al’umma ta hanyar aiwatar da dokokin zirga-zirga. Saboda haka, tana buƙatar haɗin kan al’umma wajen ganin an cimma wannan buri.