Rundunar ‘Yansanda ta jihar Kebbi ta samu nasarar cafke bakin haure Mutane 165 wadanda suka fito daga kasashen Afirka daban-daban.
Acewar, CSP Nafi’u Abubakar, an gano wadanda ake zargin ne a wasu ɗakunan kwana uku da ke Unguwar Kuwait a Birnin Kebbi.
- NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
- Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno
A yayin gudanar da binciken, an tantance bakin hauren cewa, sun fito ne daga kasashen Burkina Faso, Jamhuriyar Benin, Jamhuriyar Nijar da Ivory Coast.
CSP Abubakar ya kara da cewa, an mika wadanda ake zargin ga jami’an hukumar Kula da Shige da fice ta Nijeriya (NIS) reshen jihar Kebbi don ci gaba da bincike.