ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Wanda Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani, Shi Ma Sai An Hukunta Shi – Gwamna Sule 

by Sulaiman
1 year ago
Sule

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sha alwashin zakulo duk wadanda suke da hannu a rikincin da ya barke a garin Mararraba Udege da kauyen Oduh a makon da ya gabata.

Ya ce, “hakkin Gwamnati ne ta samar da zaman lafiya da kare dukiyoyin al’umma, don haka, duk wanda aka samu da hannu a wannan rikicin za a mika shi gaban kotu ta yi masa hukunci daidai da abinda ya aikata.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
  • Kuɗin Fansa ₦13m, Kasonsa ₦200,000: Ɗan Shekara 50 Ya Jagoranci Garkuwa Da Ɗansa Da Iyalansa 

“Abin bakin ciki ne mutanen da suke ‘yan kabila daya, Asali daya, Uwa daya, Uba daya amma suna kashe junansu saboda son zuciya da kwadayin abin Duniya.

LABARAI MASU NASABA

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

“Wannan jahilci ne, babu yadda mai hankali zai yarda ya kashe dan uwanshi saboda abin duniya.

“Babu wata kabila da ake kira Afon dutsi ko Afon kasa. Duk sunansu AFO.  Ya kuma janyo hankalin matasa da su daina yarda ‘yan siyasa batagari na amfani da su wajen neman biyan bukatar kansu, suna sanya su kashe junansu ko kona gidajen al’umma.”

Gwamna Abdullahi Sule ya kara da cewa, ya je kasar Sin don tattaunawa da kamfanin hakar Ma’adanai na ‘Juling Lithium Nasarawa Lithium Project’ a birnin Beijing, don ganin yadda kamfanin zai sake habaka basirar ma’aikata Leburori da ke aiki a kamfanin da ke Udege. Ganin cewa, ma’aikatan fiye da shekaru 20,  aikin leburanci kawai suke yi babu ci gaba, don haka, dole a samu sauyi.

“Na tattauna da manyan Shugabannin kamfanin Shneyen. Nace sama da shekara 20 kuna hakar ma’adinan Tantalaye a Udege kuna tafiya da shi. Amma mutanen Udege baya ga aikin leburanci babu wani aikin da kuka basu. saboda haka, yanzu me zaku yi Wanda matasan gurin zasu samu aikin yi? Wannan maganar ta tabasu sosai. Nan take suka ce, za su gina katafaren kamfani da za a dauki matasa aiki a koyar dasu ilimin yadda ake sarrafa Ma’adinai da sauransu.

“Don haka, bai dace a kawo hargitsin da zai yi sanadin kulle wannan kamfani da wannan alherin da ke shirin zuwa wannan yankin ba, saboda banbancin siyasa.”

Shima a nasa jawabin OSu- Ajiris na Udege Mbeki Dr. Alhaji Halilu Bala ya yi godiya ga Gwamna Abdullahi Sule da ya yi tattaki da tawagarsa yazo ya gane wa idanunsa kuma ya dauki matakin da ya dace.

Sarkin yayi kira ga wadanda aka yi wa barna da su kara hakuri, doka za ta yi aiki kan duk wanda aka kama da hannu kan tayar da rikicin.

Sule
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe
  • Sulaiman
    GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara
  • Sulaiman
    Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026
  • Sulaiman
    Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

MASU ALAKA

Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
Labarai

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan
Manyan Labarai

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Next Post
Gobara Ta Tashi A Wata Makarantar Allo Ta Hallaka Mutum 17, Ta Jikkata 16 A Zamfara

Gobara Ta Tashi A Wata Makarantar Allo Ta Hallaka Mutum 17, Ta Jikkata 16 A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026
‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

‘Yan Ƙasar Turkiyya Sun Nuna Jarumta Da Kare Dimokuraɗiyya Mafi Girma A Tarihi – Erdoğan

July 15, 2026
Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

Majalisa Ta Ba da Tallafin ₦50m Ga Iyalan Malamai Da Jami’an Tsaro Da Aka Kashe A Aikin Ceto A Oyo

July 15, 2026
Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

Xi Ya Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Bukatun Jama’a Yayin Rangadin Da Ya Yi A Shanghai

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.