Kayayyakin Sin sun yi suna a duniya, saboda ingancinsu da farashinsu mai rahusa. Wannan halayya ita ake gani a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI. Manhajar AI da kamfanin DeepSeek na kasar Sin ya gabatar, mai suna DeepSeek-R1, tana da ingancin da ya kai matsayin koli, amma da kudi kalilan ake tabbatar da gudanarta, lamarin da ya ja hankalin mutanen duniya.
A nasu bangare, kwararru a fannin fasahar AI na kasashen Afirka sun yabawa manhajar, ganin rawar da take takawa ta fuskar tabbatar da daidaiton fasahohi tsakanin kasashen duniya.
- ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
- NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu
Wani masanin fasahar AI dan kasar Afirka ta Kudu mai suna Kennedy Chengeta, ya ce, idan wani kamfani na son yin amfani da fasahar AI, za a bukaci ya zuba dimbin kudi wajen shirya kayayyaki da horar da ma’aikata, sai dai yanzu manhajar DeepSeek-R1 za ta ba shi damar tsimin wadannan kudade. Kana Alfred Ongere, mai kamfanin AI Kenya, ya ce, yadda kamfanin DeepSeek ya samar da manhajar DeepSeek-R1 ga kowa maimakon boye shi, zai ba kamfanonin kasashen Afirka damar kirkiro manhajojin AI na harsunan Afirka, bisa amfani da DeepSeek-R1 din a matsayin tushensu.
Dalilin da ya sa za a iya gabatar da fasahohi da tsare-tsaren tushe na wannan manhaja, kuma ba tare da karbar kudi ba, shi ne, na farko, manufar kamfanin DeepSeek na kasar Sin, inda mai kamfanin mista Liang Wenfeng ya ce duk wata nasarar da shi da mutanensa suka cimma, sun samu ne bisa “tsayawa kan kafadar magabata wadanda suka gabatar da fasahohin ba tare da rufa-rufa ba”, saboda haka kamfanin shi ma ba zai yi tsumulmula ba. Yayin da dalili na biyu shi ne, cikin DeepSeek-R1 an yi amfani da tsarin gudanar da manhaja mai inganci, wanda ya rage bukutar dake akwai kan ingantaccen na’urar Chip, da yawan gudanarta, ta yadda kudin da kamfanin DeepSeek ke kashewa wajen sarrafa manhajarsa ya ragu, idan an kwatanta da na wasu manyan kamfanonin AI na kasar Amurka.
Sai dai wani abu mai ban sha’awa shi ne, kamfanin DeepSeek ba zai iya samar da tsarin gudanar da manhaja mai matukar inganci ba tare da “damar” da kasar Amurka ta samar masa ba. Saboda kayyadewar da kasar Amurka ta sanya wa bangaren fitar da kayayyaki masu kunshe da fasahohin zamani, kamfanin DeepSeek na Sin ya kasa samun na’urar Chip mafi inganci da babban kamfanin sarrafa Chip na kasar Amurka Nvidia ya samar, lamarin da ya tilasta shi daukar dabarar inganta tsarin gudanar da manhaja. A nashi bangare, Zack Kass, tsohon babban jami’in kamfanin OpenAI na kasar Amurka, ya takaita batun kamar haka: Kasar Amurka na neman amfani da takunkumi wajen hana Sin samun ci gaba a fannin fasahar AI, sai dai takunkumin ya kara kaimi ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na Sin a kokarinsu na kirkiro sabbin fasahohi.
Bisa wannan batu za mu iya ganin cewa, a wannan zamanin da muke ciki na samun ci gaban fasahohi cikin matukar sauri, ya kamata a kara nuna ra’ayi na bude kofa, da karfafa hadin gwiwa da cudanya da juna, maimakon nuna ra’ayin ‘yan mazan jiya da kasar Amurka da wasu kasashe suke yi, inda suke neman yin amfani da takunkumi da babakere wajen kiyaye fifikonsu a bangaren kimiyya da fasaha, matakin da ya raunana su ta fuskar karfin kirkiro sabbin fasahohi, abin da ya zama “Don auki ake yin kunu, ya koma ya rasa auki” ke nan.
Sai dai ko da yake batun nan ya kasance gargadi ga kasar Amurka da wasu, zai karfafa gwiwar ‘yan Afirka. A ganin masaniyar fasahar AI ‘yar kasar Ghana Rashida Musa, yadda kamfanin DeepSeek na Sin ya kawar da shingen da aka dasa masa ta hanyar kirkiro sabbin fasahohi, zai zama abin koyi ga matasan kasashen Afirka, don su raya kansu bisa shawo kan matsalolin da suke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp