• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabbin Matakan Harajin Amurka: Da Alama Kaikaiyi Zai Koma Kan Mashekiya

by CGTN Hausa and Sulaiman
9 months ago
Amurka

Ko ina ka duba kwana nan, ana ta magana a kan yadda sabbin matakan gwamnatin Donald Trump ke tayar da zaune tsaye a harkokin kasuwancin duniya. To, sai dai kuma ga dukkan alamu, kaikayi zai koma kan mashekiya sakamakon wata sanarwar da kungiyar manoman Amurka ta fitar a kan yadda lamarin zai dagula lissafin ’ya’yanta.

An yi hasashen cewa, amfanin gonar da Amurka ta fitar waje a shekarar 2024 ya kai na dala biliyan 170.5, kuma kasashen da Trumph ya ayyana kara wa haraji: Sin, da Mexico da Canada su ne kan gaba wajen sayen amfanin gonar na Amurka da kashi 49.9 cikin 100. Don haka, manoman suka ce, sanya karin haraji kan kasar Sin da sauran manyan masu shigo da amfanin gona na Amurka zai kawo masu cikas.

  • ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
  • Matsalar “Fentanyl” Ba Laifi Ne Da Amurka Za Ta Iya Dora Wa Wasu Ba

Duk da Trump yake, a ranar Talatar nan, ya ce zai dakatar da harajin kashi 25 a kan Mexico da Canada na tsawon wata guda, amma kuma kasashen ba za su amince ba domin sun san Trump “mage ne mai kwanciyar daukar rai”.

Manoman Amurka da suka koka da lamarin a karkashin kungiyarsu ta cinikayyar amfanin gona, sun ce, dama suna ta faman kaka-ni-ka-yi a cikin tsadar fitar da kayayyaki, da raguwar farashin amfanin gona, kana ga kalubalen samar da wadataccen abinci a duniya. A yanzu kuma, karin harajin na Amurka zai kara dagula lamarin a yawancin yankunan karkarar Amurka saboda su ma kasashen da abin ya shafa ba za su rungume hannu su zura ido suna kallon ruwa kwado ya yi masu kafa ba.

A cewarsu, “karin harajin zai kuma jefa manoman Amurka cikin hasara sannan ya bai wa abokan gasarmu na Kudancin Amurka da sauran sassan duniya damar yi mana fintinkau ta hanyar karbe cinikinmu daga abokan kasuwanci saboda tsadar da kayanmu za su yi.”

LABARAI MASU NASABA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

“Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in ji sanarwar.

Tabbas! abin da manoman suka fada gaskiya ne, domin ko a shekarar 2018, karin harajin da Amurka ta kakkaba a kan kayayyakin kasar Sin, ya janyo kasar ta Sin wadda a baya ita ce ta fi shigo da wake na Amurka, ta sanya karin harajin kashi 25 cikin 100 na ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa. Kuma a yanzu ma, Sin ta lashi takobin mayar da martani inda tuni, a farkon makon nan ta fitar da sanarwa daga ma’aikatar cinikayya da ma’aikatar kudi a kan fara aiwatar da martaninta ga Amurka.

Daga ciki, kasar Sin ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga Fabrairun nan. Sannan, Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH da Illumina a cikin jerin kamfanonin da ba su da tabbas. Kana ta shigar da kara a gaban Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, watau WTO. Bugu da kari, Sin ta hana fitar da wasu sinadarai masu muhimmanci da ake amfani da su wajen hada kayayyakin lantarki da na karafa.

Fitina dai a kwance take, kuma la’ana tana kan duk wanda ya tayar da ita! (Daga Abdulrazaq Yahuza Jere)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu
Daga Birnin Sin

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Next Post
Mun Hana Kai Wa ‘Yan Bindiga Burodi Ba Hana Sayarwa Ko Gasawa Ba – Dauda

Dauda Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.