A kwanan baya, kasar Amurka ta kakaba wa kayayyakin kasar Sin da ake neman shigar da su cikin kasuwanninta karin harajin kwastam na kaso 10%, bisa dalilin wai Sin na sayar da magani mai suna Fentanyl a kasar.
Hakika maganar Fentanyl din wani batu ne da kasar Amurka ta dade tana kokarin ruruta shi, inda wasu ‘yan siyasar kasar ke neman dora laifin yadda mutanen kasar ke amfani da maganin a matsayin miyagun kwayoyi kan kasar Sin, cewa wai “Sin na samar da sinadarin hada maganin Fentanyl, wanda aka sarrafa shi zuwa miyagun kwayoyi a Mexico, tare da kai su cikin Amurka”. Sa’an nan Amurka ta fake da wannan dalili tana kakaba wa kamfanonin Sin takunkumi, har ma ta kaddamar da matakin hukuncin haraji a wannan karo.
Sai dai a ganin Farfesa Li Haidong na jami’ar diflomasiyya ta Sin, gwamnatin Amurka ta yi sakaci wajen sa ido kan yadda ake amfani da maganin Fentanyl a cikin gidanta, abin da ya sa batun ya zama wata matsalar da ake fuskanta a kasar. Sa’an nan, da gwamnatin kasar Amurka ta ga ta kasa magance matsalar daga tushe, sai ta fara dora laifi ga sauran kasashe da suka hada da Sin da Mexico, don nuna wa jama’arta cewa tana daukar mataki. Ban da haka, ta mai da maganar Fentanyl a matsayin wani dalili na daukar matakin karin haraji kan kayayyakin kasar Sin. (Bello Wang)