Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar, tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl. Bayan haka, nan take kasar Sin ta sanar da daukar matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka domin kare hakki da moriyarta yadda ya kamata. Saan nan, a ranar 4 ga wata, Sin ta gabatar da cewa, tun daga ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 2025, za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka. A sai daya kuma, kasar Sin ta shigar da kara kan matakan da Amurka ta dauka na karin haraji a bangaren sassanta rikici na hukumar kula da kasuwanci ta duniya, watau WTO. Lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana maraba da shawarwarin da za a yi bisa adalci, kana, za ta mai da martani kan takunkumin da aka sanya mata, domin kare hakkinta na neman ci gaba.
Abubuwan da suka faru cikin shekarun baya bayan nan, sun nuna cewa, daga karshe dai, kasar Amurka ce za ta yi fama da mummunan tasirin yakin haraji da ta tayar. Bayan matakan cin zalin ciniki da ta dauka kan kasar Sin, ba gazawa wajen cimma burinta na farfado da aikin kere-kere da rage gibin kudi kadai Amurka ta yi ba, har ma da rasa damarta a muhimman kasuwannin kasa da kasa.
Matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka da kasar Sin ta dauka, su kasance matakai na wajibi domin dakile raayin Amurka da fifiko da hana yaduwar kariyar ciniki, ta yadda za ta kiyaye hakkinta na neman ci gaba yadda ya kamata, tare da kare tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da kuma kaidar adalci ta kasashen duniya. Babu wanda zai ci nasara cikin yakin ciniki da yakin harajin kwastam. (Mai Fassara: Maryam Yang)