Wani Jami’in ɗansanda mai suna, Dogara Akolo-Moses, da ke aiki a ofishin ’yansanda na yankin Mada a Jihar Nasarawa, ya kawo ƙarshen rayuwarsa ta hanyar harbe kansa da har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗansandan, yana aiki ne a Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon ta jihar Nassarawa.
- Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa
- Zargin Safarar Kananan Yara: Gwamnatin Kano Ta Karbi Yara 59 Da Aka Kama A Hanyar Zuwa Nasarawa
Shaidu sun bayyana cewa jami’in ya harbe kansa da bindigar ne bayan da ya shiga wani ɗaki, sai ƙarar sautin harbin ya ɗauki hankalin abokan aikinsa, suka garzaya ɗakin, inda suka same shi kwance cikin jini tare da bindiga a gefensa.
Sai dai har yanzu ba a san dalilin jami’in na hallaka kansa ba, kamar yadda kakakin rundunar ’yansandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya shaida yayin tabbatar da faruwar lamarin.
Ramhan, Ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da gudanar da binciken gano musabbabin da ya sa jami’in ya yanke wannan mummunan mataki na kashe kansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp