Kwanaki uku bayan da Arsenal ta doke zakarun gasar Firimiya Manchester City a wasan mako na 24 na gasar Firimiya ta kasar Ingila, sai ga shi a daren jiya Laraba ita ma ta gamu da gamonta in ji bahaushe yayin da Newcastle ta jefa kwallo biyu a ragar yaran na Arteta a wasan na kusa da na ƙarshe na kofin EFL wanda a baya aka fi sani da Carling Cup.
Tun a shekarar 1993 rabon da Arsenal ta lashe wanna kofi, Jacob Murphy da Anthony Gordon ne suka jefa ƙwallaye biyun da suka yi waje da Arsenal a gasar ta EFL.
- Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu
- Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates
Yanzu ƙungiyar ta birnin Landan za ta mayar da hankalinta wajen sauran kofunan da suka rage wato Firimiya Lig da kuma Gasar Zakarun Turai wadda suke neman lashewa a karo na farko a tarihinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp