Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci sojojin Nijeriya da su tabbatar da sun kawo karshen matsalar rashin tsaro nan da karshen shekarar 2025.
Umarnin wanda ministan tsaro, Abubakar Badaru, ya sanar da ita ta cikin wani bidiyo da ya yada.
- Binciken CGTN: Tasaruffi A Cikin Sanyi Ya Daukaka Sunan Harbin Da Nuna Yakini Ga Habakar Tattalin Arzikin Sin
- Nijeriya Na Da Dimbin Dukiyar Da Tinubu Zai Rika Tafiye-tafiye Zuwa Kasashen Waje – Minista
Badaru ya ce, yaki da kowace nau’in garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’adda zai ci gaba da fadada biyo bayan wannan umarnin na Tinubu.
A fadinsa, ‘yan fashin daji na ta arcewa kuma kokarin kawo karshen matsalar tsaro ba zai kammalu ba har sai an tabbatar an gama da kowani dan ta’adda.
“Yan bindiga a halin yanzu na ta arcewa, amma sojoji ba za su sarara ba har sai mun kawo karshen wannan lamarin. Shugaban kasa ya bayar da umarnin na musamman da a kawo karshen matsalolin tsaro a kowani bangare na kasar nan zuwa nan da karshen wannan shekarar.
“Babban shugaban sojoji da Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro (NSA) suna aiki ba dare ko rana wajen tabbatar da wannan matakin, kamar yadda kuke gani muna sanya kumaji ga dukkanin rundunoni.
“Sannan, an janye takunkumin hako ma’adinai a Zamfara, sannan wannan dalilin ne ya sanya muke ganawa a yau domin duba dukkanin bangarorin, inda muke da matsalar tsaro sosai sai mu ga yadda za mu kwato ayyukan,” Badaru ya shaida.