Masarautar Mubi da ke arewa maso gabashin Nijeriya, wacce ke da nisan kimanin kilomita 220 daga Yola fadar Jihar Adamawa, baya ga kasancewar masarauta ita ce masarauta ta biyu mafi girma da shahara a jihar, masarautar ta kuma shahara ta fannonin noma, kiwo da kasuwanci.
Mazauna masarautar wacce al’ummar Fulani suka kirkira a karni na 18, ta kasance karkashin Daulan Mandarawa, na lokaci mai tsawo kafin zuwa Jihadin Shehu Usmanu Ibn Fodiyo da ta koma karkashin Daular Musulunci da Modibbo Adama ya jagoranta a yankin.
- Ziyarar Babbar jami’ar Lithuania A Taiwan Shirme Ne
- Tinubu Ga Peter Obi: Ka Gargaɗi Magoya Bayanka Kan Ɓata Min Suna
A shekara ta 1820 ne, jama’ar Mubi da kiwayen masarautar suka mika wuya ga Jihadin Shehu Usmanu bisa jagorancin Modibbo Adama, wanda daga baya ake kira da ‘Masarautar Fombina Adamawa.
A shekarar 1890, masarautar Mubi ta nemi ta balle daga masarautar Fombina lokacin da Marigayi Lamido Zubairu ke kan garagar mulkin masarautar Fombina a matsayin sarki.
Da karfin tsiya, Turawan Jamus suka amshi iko da masarautar a shekarar 1903, suka kuma rike masarautar a matsayar ita ce cibiyar gudanar da mulkin Jamus-Kamaru har lokacin da Turawan Birtaniya suka kwace iko da masarautar a shekarar 1914.
Masarautar Mubi da kiwaye ta kasance karkashin Birtaniya-Kamaru bisa hadin gwiwar kasashen Turawa har a shekarar 1922.
A shekarar 1961, masarautar Mubi ta kasance cikakkiyar bangare daga cikin bangarorin kasar Nijeriya.
A tsawon wadannan shekaru, masarautar Mubi na amsar umurni daga masarautar Fombina, domin kuwa masarautar Lamido Adamawa (Fombina), ke nada hakimi a masarautar ta Mubi a lokacin tsohon tsarin gudanarwar mulkin Nijeriya, kafin da bayan kirkiro da sabbin jihohi ciki har da jihohi daga tsohowar Jihar Gongola a shekarar 1976.
Daga lokacin ne kuma, Gwamna Abubakar Sale Michika, a shekarar 1989, ya mayar da masarautar ta koma mai cin gashin kanta, ta yadda sarkin masarautar ya zama mai martaba na daya mai makon hakimi.
A lokacin guda kuma aka nada mai Martaba Isa Ahmadu a matsayin sarki mai daraja ta daya na masarautar Mubi, da ta hada kananan hukumomin Maiha, Hong, Michika, Madagali, inda masarautar ke nada musu hakimai a yau.
A shekarar 1991, aka nada Alhaji Abubakar Isa Ahmadu a matsayin Mai Martaba Sarkin Mubi, bayan rasuwar Mahaifinsa, to sai dai duk da samun cin gashin kai da masarautar ta samu daga masarautar Fombina, masarautar Mubi na da kyakkyawan alaka da dangantaka ta kut-da-kut da masarautar Fombina a tsawon wadannan shekarun.
Wani muhimmin abu game da masarautar Mubi shi ne, rikici ko tashin-tashinan da ake samu tsakanin manoma da makiyaya ko tsakanin kabilu a wasu yankunan Jihar Adamawa ba a taba samun irinsa a masarautar Mubi ba. Garin Mubi bai taba fuskantar wata barazanar da ta wuce ta Boko Haram a shekarar 2014 ba.
Zaman lafiya da kwanciyar hankali hadi da fahimtar junan da masarautar ta samar a tsakankanin jama’a da kabilu mabambanta ya haifar mata ci gaban da zama cibiyar kasuwancin jihar, kuma ta ci gaba da zama babbar kasuwar Shanu ba kawai a arewa maso gabas ko Nijeriya ba, kasuwar Shanu ta Mubi ta kasuwace ta kasa da kasa.
A masarautar Mubi ta yau da ta hada kananan hukumomi biyar, ba a taba samun wani manomin da ya yi noma kan burtalin shanu ba, saboda haka makiyaya ba su taba shiga gonar wani manomi ba, kasantuwar suna da hanyoyin da za su wuce da shanunsu su tafi kiwo ko kaura daga wuri zuwa wani wuri, kamar yadda makiyaya suka saba yi.
To sai dai, akwai masu ganin lokaci ya yi da za a samu karin kirkiro wata masarauta mai daraja ta daya daga yankin, lamarin da masu tunanin ke ganin zai taimaka ga samun saukin gudanarwa ga gwamnatin jiha dama ita kanta masarauta.
Da yake magana game da masarautar Mubi, Hassan Muhammad Oscer, ya ce “Babu abin da za mu ce game da mai martaba sai godiyar Allah, shekaru 31, yake a matsayin Sarkin Mubi ba mu taba samun rikici ya faru a tsakaninmu kabilusa na Fulani a yankin masarautarsa ba.
“Mutum ne wanda yake kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ko rikici tsakanin makiyaya da manoma ba a taba samu ba tun da aka kirkiri masarautar Mubi, haka kuma ba a taba samun damuwa tsakanin Fulani da sauran kabilu ba.
“Tun lokacin da ake tura hakimai daga masarautar Lamido, ba a samun matsala a yankin, daga lokacin da masarautar ta samu babban sarki mai daraja, sarkin ya maida hankali wajan hade kan al’umman yankin, muna zaune lafiya da fahimtar juna,” in ji Hassan Oscer.
Da yake magana kan batun raba masarautar kuwa Oscer cewa ya yi “Ba mu da wata matsala da sarkinmu, amma idan gwamnati ta ce tana da niyyar za ta yi abinta, babu mutumin da ya isa ya hana gwamnati, domin mu kanmu da sarakunan gargajiya malumanmu da fastocinmu ita ta ajiyemu muna karkashinta ne.
“Saboda haka idan gwamnati ta ce za ta yi ya rage mata da ‘yan majalisar dokoki, ba mu da muke karkashin Sarkin Mubi ko karkashin sarakunan gargajiya ba,” in ji Hassan Oscer.