Rahotanni sun ce, mataimakiyar ministan sufuri da sadarwa na kasar Lithuania, ta jagoranci wata tawaga zuwa yankin Taiwan, domin gudanar da ziyarar kwanaki biyar tun daga ranar 7 ga watan nan na Agusta.
A yayin da yake mayar da martani, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Alhamis cewa, kasar Sin ta yi kakkausar suka, ga yadda rukunin masu adawa da gwamnatin kasar Sin na Lithuania, ke keta hurumin kasar Sin da gangan, da kuma tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce babbar ka’idar dangantakar kasa da kasa, kuma ginshikin siyasa ne ga kasar Sin, a fannin raya dangantakar dake tsakaninta da sauran kasashen, ciki har da Lithuania.
Ban da wannan kuma, game da furucin da sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss ta yi a ranar 10 ga wata, inda ta yi Allah wadai da karuwar matakan da kasar Sin ke dauka a mashigin tekun Taiwan, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, bangaren Birtaniya, ya yi watsi da gaskiyar lamarin, da kuma sauya fari da baki, kana da yin kalamai marasa ma’ana game da halastattun matakan da suka dace kasar Sin ta dauka, don kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan ta.
Wang ya kara da cewa, bangaren Sin bai gamsu da hakan ba, kuma yana nuna adawa da hakan, ya kuma nuna matukar takaicinsa game da kalaman bangaren na Birtaniyya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)