A yau shafin Taskira na wannan makon zai yi duba ne game da matsalar da ke afkuwa ga wasu samarin bayan kai kudi na gani ina so.
Wasu daga cikin samari na daura damarar yin aure, wanda kuma har takan kai da an tura iyaye kai kudin na gani ina so, wanda hakan ke nuni da shaidar an bawa saurayi yarinyar da yake so bisa al’adar Malam Bahaushe.
- Shin Kana Tuna Wadannan Idan Za Ka Aikata Zunubi?
- Wani Yaro Dan Shekara 12 Ya Harbe Mahaifiyarsa ‘Yar Nijeriya A Amurka
Wanda kuma hakan ke sa a saka ranar auren masoyan zuwa tsahon wani lokaci.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, saka lokaci mai tsaho na aure kan janyo targarda na rugujewar yin auren ga wasu matasan.
Wanda bayan shudewar wasu lokuta da saka rana, iyayen yarinyar kan mayar da kudin auren ba tare da dalilin komai ba.
A tawa fahimtar ana samun wannan matsalar ta kowanne bangare, ga su iyayen yarinyar da yarinyar har ma da shi kansa saurayin.
Wasu iyayen yarinyar na zaba wa diyarsu namijin da za ta aura ta hangen abin da saurayi yake da shi, musamman wajen ganin yadda yake kashe wa diyarsu kudade masu yawa, yayin da suka samu wanda ya fi shi sai su yanke shawarar mayar wa da yaron kudinsa, musamman in muka yi duba da wannan zamani.
Wasu kuma ba haka bane, bunciken da suka yi ne akan saurayin tun a farko bai yiwu ba, sai bayan lokacin da aka saka ranar aure, sa’annan suke kara samun wasu bayanai a kan yaron, wanda suke ganin yarinyarsu sam! ba ta dace da tsarin yaron ko ahlin yaron ba.
Yayin da wasu kuma ke kallon yawan dage-dagen auren da ake yi ke sawa su canja ra’ayinsu gudun kar yarinyarsu ta tsufa a gida.
Wasu kuma ganin babu muhallin zama ko kadan ke sawa su fasa bawa yaron ko da kuwa yana da sana’ar yi.
Wasu kuma rashin aikin yi da rashin muhalli ke sawa su fasa ba da diyarsu, Wasu kuma umarnin ‘Yarsu kawai suke bi, musamman in ta shiga babbar makaranta sai ta ga sam! ba ajinta ba ne, ko kuma idan ta sami wanda ya fishi sai ta nemi a fasa, su kuma iyayen ba sa duban ka da su zama kananun mutane idan suka maida kudin, amma a haka za su mayar gudun ka da su bata wa diyarsu rai.
Ta bangaren samarin kuwa wasu iyayen saurayin ke sa buri cikin auren wanda har takan kai a rasa lokacin gabatar da auren ko da kuwa an saka ranar auren, akan yawaita daga lokacin auren har ma ya zo ya wuce ba a yi ba, sakamakon burin da aka daukarwa bikin har zuwa lokacin bai gama tabbatuwa ba, har ta kai ga iyayen yarinyar sun gaji da jira sai su fasa.
Wani saurayin kuma ya gina soyayyar ne bisa karya, abin da bai da shi ya nuna cewar yana da shi alhalin bai da komai, wani sa’in ma iyayen hayo su yake ba nasa ba ne, komai nasa na aro ne ya ki bayyana kansa a matsayin da yake da shi, wannan ya sa a duk lokacin da gaskiya ta bayyana sai iyayen yarinyar su fasa bawa yaron, domin ko kusa bai dace da diyar su ba.
Wani kuma saurayin yakan boye wasu dabi’unsa ne wanda su kansu iyayensa ba su san yana da dabi’un ba, musamman ta fannin addini ko wasu munanan dabi’un da basu dace da shi ba, a duk lokacin da iyayen yarinya suka gano hakan sukan fasa bawa saurayin diyarsu.
Akwai abubuwa da dama wanda ke faruwa har takan ja a mayar da kudin na gani ina so, wanda wajen ya yi kadan a bayyana shi, sai dai a fade su a takaice. Ko shin laifin waye tsakanin Iyayen yarinyar, da yarinyar da shi saurayin?
Ko me yake jawo hakan? Ta wacce hanya za a magance matsalar?
Wannan ya sa shafin Taskira ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa inda suka fadi nasu ra’ayoyin kamar haka:
Samu labarin hakan ya faru za ka samu ne wadda ya zo daga bayan ya fi na farkon kudi, ba za ka taba jin an ce na farkon ya fi kudi ba, a nawa tunanin laifin iyaye ne, domin ita yariya canza ma ta tunani ba abu bane me wahala, su ya kamata su zama dattijan kwairai wajen rike alkawari da amana, ko da ace ita yariyar ce wani ya rikitata da kudi su ya kamata su nuna ma ta sudin dattijen kwarai ne ba sa magana biyu, amman iyayen yanzun sai ka samu sun ma fi yaran zakewa da nuna rawan kafa, sune suke kara karfafa wa yariyar guiwa a irin wannan lokacin, duk saboda kwadayin abun duniya da dogon buri, Ina kira ga iyaye da su guji kwadayin abun duniya wajen ba da aure, ya dace su dinga duba hankali da nutsuwa tare da iya neman nakai ne kawai ga wadda ya zo neman auren gare su, su kuma matasa shawarata garesu su dinga sanin gidan da za su nema aure, kuma ban da karya ka nuna ainihin kalarka idan za a soka a soka a haka, ban da jimawa wajen neman auren idan har auren za ka yi da gaske babu amfanin jimawa ba tare da an yi auren ba, Allah ya sa mu dace.
Hafsat Yusuf Muhammad daga Jihar Kano:
Da farko saurayin da aka bashi yarinya zai aure ta daga baya iyayenta suka fasa to wani abu ne mai mahimmanci ya sa aka fasa sabida babu iyayen da za a kawo kudin ‘yar su daga baya su ce sun fasa babu dalili misali; saurayin ko ba shi da kunya ko kuma yana wulakanta musu ‘yar su, ko kuma dan iska ne yana bun matan baza ko sun yi buncike sun ga ba shi da sana’ar da zai ruke ‘yar su to za su ce ya zo ya karbi kudinsa.
Gaskiya wani lokacin laifin saurayin ne, kana son budurwa ka dinga yi ma ta kyauta kana ganin girman iyayenta da kowa nata amma sai ki ga yana yi musu kallon wulakanci. Abin da yake jaho hakan shi ne; rashin tarbiyya ne da kuma wulakanta dan Adam ko ya fi su kudi ne shi yasa.
Hanyar da za a magance matsalar shi ne samari suna ganin girman iyayen matar da za su aura ita ma budurwar tana ganin girman nasa to zamu sami saukin gyarawa Allah ya sa mu dace.
Shawarar da zan bawa mu matasa shi ne; mu dinga ganin girman iyayen mu kar mu dubi ni dan wane ne ke ma kar ki dubi ‘yar wane ce kuma mu rage karya dan ita ma tana ba mu matsala sosai sai dai Allah ya sa mu dace.
Sunana SaNaz Deeyah:
Babu abin da zai saka a maida kudin aure ba tare da wani dalili mai karfi ba, ni a mahangata, sa rana mai tsawo kan jawo gundura tsakanin saurayi da budurwa, fada ce-fada ce da dai sauransu.
Wanda mafi akasari shaidan ne, a wasu lokutan kuma iyaye sukan mayar ne saboda ganin cewar shi wancan bai shiryawa aure ba, ga kuma wani ya fito wanda a shirye yake.
Sau tari in aka bibiya za a ga laifin iyaye ne, domin ita zuciyar mace rauni ne da ita, ta yuwu wani wanda ya fi wancan yazo, amma su iyaye bai kamata ace, sun yi karamar magana ba in har shi saurayin ba shi da wani laifi.
Rashin kyakykyawar fahimta da kuma kyakykyawan zato sune kashin bayan matsalar.
Ta hanyar fahimtar juna, da kuma tattauna akan matsalolin ba tare da an kawo zuciya kusa ba.
Ni dai a shawarce duk wanda zai nemi aure a wannan ƙarnin ya tabbatar yana da tsayayyen aiki ko sana’a, da kuma muhalli sannan ya tabbatar da ya shirya, sannan ya tunkari iyayen yarinya, ta yadda za a saka biki a watanni kadan.
Fauziya S. Madaki daga Jihar Kaduna:
Toh hakan yana iya kasancewa laifin saurayin, dan wani ya kan kai kudin aure yayi shekaru ba tare da ya kara yin wani yunkuri ba, saboda yana tutiyar ya kai kudinsa ba za ta iya saurarar wani ba, wasu iyayen kuma kwadayi ke sa su mayar da kayan, da zarar sun ga wanda yafi na farkon abun hannu sai su watsar da maganar farkon ko da bai musu laifin komai ba.
Kowanne bangare yana da irin nasa laifin, shi saurayi da zarar ya kai kudin nagani ina so yayi kokari a tsayar musu da lokaci, idan kuma bai shirya ba ya yi hakuri ya bari sai ya shirya don wasu iyayen suna kallon hakan a matsayin batawa ‘yar su lokaci, su kuma iyayenmu da zarar kun karbi kudin saurayi to kuyi hakuri ku tsaya tsayin daka wajen ganin kun cika alkawari batukar ba kun gano wani aibu tattare da shi ba.
Kwadayi da son zuciya sune kaso mafi tsoka a ciki da zarar mun janye kwadayi da son zuciya toh ita kanta rayuwar auren za ta zama mai tsabta.
Ta hanyar komawa wajen yin aiki da hadisan Manzon Allah (s.a.w) da koyi da sahabbansa wajen neman aurensu da rayuwar auren gaba daya. Sannan iyaye da mu ‘yanmata mu cire dogon buri, kwadayi, da sauransu.
Hassana Yahaya Iyaya (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Maganar gaskiya wani lokaci wasu iyaye da zarar sun ga wani wanda yafi waccan na farko dan shi ya zo wajen ‘yarsu tofa daga nan sai kwadayin abin duniya ya rude su su fasa ba wa na farkon karshe ta kuma shi ma na bayan da zo ya gudu ayi ba wan ba kaninan.
Laifi na iyayen ne wannan domin kuwa kwadayi ai mabudin wahala ne.
Iyaye dai su fadaku su san aure fa ba a bin wasa ba ne, ko suma in kayi wa na su dan ba za su ji dadi ba. ayi hakuri duk wanda ya zo da niyar aure a bashi in har ba wani dalili ne mai karfi ba ya hana.
Nawa ganin abin da ke jawowa bai wuce ruwan ido ba, sai kuma kwadayi ato.
Eh! gaskiya kin ga dogowar sa ranar nan ma na jenyowa har iyaye su ga ji, su mai da kudin ganin an jingine masu ‘ya, wani kuma dama can babu sa’a shiyasa tunda wasu samarin har adashi suke zubawa na kai kudi.
To matasa a tsaya ayi duba na tsanaki wajen samo mataye na gari, su ma ‘yan matan dai a lura da kyau wajen samawa ‘ya’ya uba na gari.
Hayatu Baba Zubair (Yaya Hayata) daga Jihar Kaduna:
Wani lokacin daga saurayin ne shi ya san cewa bai shirya aure ba kawai sai ya kai kudin gidan yarinya ayi-ayi ya fito a saka rana yaki fitowa.
Wani zubin kuma bayan ya kai kudin ne kwatsam sai ya hango wasu aibuka nata ko kuma ya canza sheka ya ki mayar da hankali wajenta ya yi ta kumbiya-kumbiya, a rasa gane inda ya dosa har iyayen su gaji su mayar masa da kudinsa.
Laifin na saurayin ne gaskiya yawanci don su suke ba da kofar ba su shirya ba.
Abin da ke janyo hakan tun asali shi ne rashin shiryawa, idan ka tashi aure to ka tafi kai tsaye idan baka shirya ba ka bari har sai lokacin ya yi. Shawarata ga matasa masu neman aure a duba da kyau a hango mai ilimi don idan ka samu wannan to duk sun hada nagartar da ake so, mai ilimi da aiki da shi da tarbiyya da addini, kamar yadda Manzon Allah SWA ya fada.
Sunana Nazifi Yarima daga Jihar Kano:
Na daya wannan abun yana faruwa ne, sakamakon ita kanta yarinyar ta samu wani wanda yafi wanda take tunanin za ta aura irin me kudin nan ya zo ya bushe ma ta kunne ko kuma sai daga baya ta ga wanda za ta aura akwai wani abu na yanayin jikinsa wanda bai yi ma ta ba, ko kuma an gano a danginsa yana da wata matsalar irin wacce ta shafi ‘Family Issue’ din nan, sai ayi rufa-rufa kawai ace a mayar masa da kudinsa a bashi hakuri.
Na biyu wannan kawai buncike ne zai tabbatar da hakan, anan ne kawai za a gano laifin waye a cikin iyayen yarinyar ko kuma yarinyar ce, ko kuma saurayin ba wanda zai tabbatar da hakan sai an yi buncike mai zurfi.
Na uku abubuwa da yawa suna jawo hakan kamar; san zuciya, hange-hange da kuma biyewa rudin shaidan.
Na hudu abun da yake jawo hakan shi ne; ta hanyar ‘Orientation’ ga iyayan yara da kuma su kansu samarin akan ma meye aure. Shawarar ita ce; kafin ka fara neman aure ko ki fara neman aure ki fara sanin meye shi kansa auren, ya ma yake, me ye auren shi kansa? Tukunnah daga nan ne ma mutum sai ya fara tunkarar Mace ko Mace ta fara tunkarar Namiji da sunan soyayya ko kuma neman aure.
Mansur Usman Sufi Sarkin Marubutan Yaki, daga Jihar Kano:
Wannan matsala ta mayar wa da saurayi kudin aure idan ya kai, tana faruwa ne ko dai saboda bincike da iyayen yarinya suka yi suka gano wadansu halaye na yaro mara kyau ko kuma mahaifansa, wa su kuwa sukan maida kudin ne saboda wani mai abin hannu ya shigo sai a fasa, sai a mayar masa kudin sa, ko ma dai mene ne ina so duk abin da iyaye za su yi su ji tsaron Allah.
Hanyar da za a magance wannan matsalar shi ne; gudanar da bincike kafin ace saurayi ya kawo kudin aure domin gudun zubewar mutumcin juna. Shawara ta ga matasa shi ne idan za su nemi aure su samu yarinya ‘yar gidan mutunci da tarbiyya ko kyakkyawa ce ko akasin haka, tarbiyya da kyawun sura abu ne mai kyau ba.