Dandalin sayar da tikiti na kasar Sin Maoyan ya kara sabbin bayanai a hasashensa game da fim din “Ne Zha 2,” inda ya bayyana cewa kudin da ake tsammanin samu daga fim din zai kai yuan biliyan 14.25 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.99, bisa jimillar kudaden da za a samu a kasar Sin.
Sabon kiyasin kudin, wanda aka sanar a jiya Litinin da dare, zai sanya fim din na kasar Sin a matsayin fim na kagaggun hotuna da ya fi ko wanne samun kudi a tarihin fina-finan kagaggun hotuna na duniya, kuma zai iya sanya shi cikin jerin fina-finai bakwai da suka fi samun kudi a tarihin dukkan fannonin fina-finai na duniya.
- Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
- Gaskiya Ta Bayyana Bayan Da Gwamnatin Amurka Ta Sanar Da Rufe USAID
Sabon hasashen da aka yi, ya zo ne kwana guda bayan da dandalin Maoyan ya kara hasashen yawan kudin da za a samu na fim din a cikin gida zuwa sama da yuan biliyan 12, wanda ya zarce kiyasin da aka yi masa na farko kimanin yuan biliyan 10.8, a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Yayin da ake sa ran fim din ya zama na farko daga kasar Sin da ya tsallaka matakin samun kudin da ya kai yuan biliyan 10, tabbas ya riga zama wani muhimmin ci gaba da aka samu a bangaren sinimar kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere).