Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare.
Kimiyya ba ta da iyaka. Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin AI na kasar Sin, ya rungumi tsarin bayyana asalin samar da fasahar. Wannan mataki, ya dace da yanayin da ake ciki yanzu.
An ga fitowar fasahar kirkirarriyar basira, kuma yadda za a yi kyakkyawan amfani da wannan karfi, batu ne dake gaban dukkan kasashen duniya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp