Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023.
Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151 na jigilar kayayyaki na kasa da sama da wuraren ajiyar kayayyaki 2,500 a kasashen waje. Haka kuma ta bude sabbin hanyoyi 168 na jiragen dakon kayayyaki na kasa da kasa a baran.
A cewar Hu Han, jami’i a cibiyar tattara bayanan da suka shafi jigila ta kasar, ingantawa kayayyakin aiki da suka shafi jigila da daukaka tsarin hanyoyin jigila sun bunkasa ware albarkatu ga bangaren da kuma hade yankunan kasa da kasa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp