Kalaman da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kan batun zirin Gaza a kwanan baya, ta sake girgiza al’ummar duniya.
A zantawarsa da kafar yada labarai ta FOX News, Donald Trump ya bayyana cewa, za a kori Falasdinawa daga zirin Gaza har abada, kuma ba su da ikon sake komawa. A wani sa’in kuma ya ce, “Ni zan mallake shi, wuri mai kyau da zan yi cinikin gidaje, ba zan kashe kudi da yawa ba game da hakan.”
- Malaman Makaranta Da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Sun Tsunduma Yajin Aiki A Abuja
- Maryam Malika Ta Buƙaci Kotu Ta Tabbatar Da Sakin Da Mijinta Yayi Mata
Trump ya hade burinsa na siyasa tare da basirarsa ta kasuwanci da cinikin gidaje wuri guda, yana son cimma burinsa ta hanyar keta hakkin Palasdinawa, kuma mambar mahukuntan kungiyar Hamas, Izzat al-Risheq ya bayyana kalaman shugaban a matsayin abin ban dariya da rashin imani da toshewar basira. Ya jadadda cewa, “Trump ya daidaita batun Gaza da halayyarsa ta dan kasuwa mai cinikin gidaje kuma ba zai cimma nasara ba ko kadan. Mu Falasdinawa ba za mu yarda da ko wane mataki na sa mu yin kaura ko kore mu daga yankin ba ko kadan.”
Zirin Gaza na matukar bukatar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci ta shirin “samar da kasashe biyu”, kuma Falasdinawa ba za su samu farfadowa ba har sai an tabbatar da bukatun nan. Ikirarin da Amurka ke yi na karbe ikon mallakar zirin ba shi da asali a karkashin shari’a da doka, mataki ne kawai da zai keta dokar duniya, har ma da tsananta halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, kuma zai sake jefa yankin cikin munanan tashe-tashen hankula marasa tabbas.
Donald Trump shugaban kasar Amurka ne kawai, don haka, ba ruwansa da yin katsalandan cikin harkokin gabas ta tsakiya da na sauran kasashen duniya. (Mai zane da rubutu: MINA)