Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta na barazanar gurgunta shirin aike da jami’an tsaro da albarkatun kasa da kuma yanayin tsaro a kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yau Juma’a a Abuja, yayin kaddamar da wani daftari na takaita rikice-rikice ta kasa da nufin cike gibin da aka samu ta hanyar aike da jami’an tsaro masu yawa ta hanyar hadin gwuiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
- Ba Laifi Don Musulmi Sun Yi Murnar Shigar Sabuwar Shekarar Musulunci
- Ya Kamata A Bar Sinawa Su Yanke Shawara Kan Al’amuran Kasar Sin
Shirin da ofishin mai bai wa shugaban shawara kan harkar tsaro da kuma hadin gwuiwa da hukumomi, zai tabbatar da cewa an samu nasara wajen dakile rikice-rikice a fadin kasar.
Buhari ya tuna cewa a lokacin da gwamnatinsa ta zo kan mulki, Nijeriya na fuskantar matsalolin rashin tsaro da dama kama daga ta’addanci da garkuwa da mutane da fashi da makami da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da satar danyen mai da sauransu.
Hakazaila, shugaba Buhari ya jinjinawa mai taimaka masa a bangaren sha’anin tsaro da kuma sauran hukumomi saboda samar da shirin, inda ya ce hakan ya nuna zimmar da ake da ita na ganin an magance rikice-rikce a fadin kasar.
Sai dai ya koka kan yadda rashin tsaron ke ci gaba sa zama babbar barazana ga tattalin arzikin kasar da kuma zaman lafiya.