Kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Kano (ALGON) ta kafa tarihi inda ta zabi shugabar karamar hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u a matsayin sabuwar shugabar kungiyar.
In ba a manta ba, mun rahoto cewa, Haijiya Sa’adatu Yusha’u ita ce mace tilo a cikin shugabannin kananan hukumomi 44 da aka zaba a watan Oktoba a karkashin jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano.
- ‘Yancin Ƙananan Hukumomi Ya Ƙara Fuskantar Koma-baya
- Za A Iya Samun Biliyoyin Daloli A Noman Zogale Da Kantu A Tekun Chadi
Haka kuma, a lokacin zaben ALGON an zabi Jamilu Abubakar Danbatta, shugaban karamar hukumar Danbatta a matsayin mataimakin shugaba mai wakiltar Kano ta Arewa; Alhaji Yusuf Imam Ogan Boye, mataimakin shugaba, Kano ta tsakiya da Abdullahi Zubair Chula, mataimakin shugaba, Kano ta Kudu.
Bugu da kari, an nada shugaban karamar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata a matsayin sakataren kungiyar.
Da yake jawabi, Gwamna Kabir Yusuf ya taya sabbin shugabannin murna, sannan kuma ya bukace su da su kara himma wajen aiwatar da ayyukan raya kasa tare da bunkasa hadin kan jam’iyyar a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp