Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), ya yi nuni da cewa; za a iya samun kudaden shiga na biliyoyin daloli a noman Zogale da Kantu a Tekun Chadi, matukar an kara inganta tsaro da zaman lafiya.
Mai wakiltar shirin a Nijeriya, Dabid Stebeson ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis da ta gabata, a taron da aka yi karo na biyar na kungiyar gwamnonin yankin Tekun Chadi da aka gudanar a garin Maiduguri na Jihar Borno.
“Yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci ta Afirka (AfCFTA), ta bayar da damar bunkasa hada-hadar kasuwanci tare da farfado da tattalin arzikin kasar, idan har aka bunkasa fannin aikin noma da kiwo.”
- Zargin China Da Bautar Da Leburori a Gonar Tumatir a Xinjiang: Mene Ne Gaskiyar Lamarin?
- Amfanin Zogale 18 Ga Lafiyar Jikin Dan’adam
Mai wakiltar shirin ya sanar da cewa, bisa hadin kai a yankin da kuma wanzar da kuduri irin siyasa, yankin zai iya magance kalubalen rashin abincin da za a ciyar da al’ummar da ke yankin.
Sai dai, Stebeson ya nuna takaicinsa kan cewa, duk da yawan sama da mutane miliyan bakwai da ke yankin, har yanzi al’ummar yankin na ci gaba da zama cikin karancin abinci.
A cewarsa, sama da mutane miliyan uku rikice-rikicen ta’addanci ya tilasta su yin kaura da daga matsugunansu.
Har ila yau, ya shawarci kungiyoyin da ke yankin; kan bukatar yin hadin kai mai karfi da samar da tsare-tsaren da za su habaka aikin noma da kiwon Kifi a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp