Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan rasuwar dattijo ɗan kishin ƙasa kuma tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Tarayya, wato Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru 97.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Cif Clark a matsayin “gwarzon ɗan ƙasa, mai fafutikar tabbatar da adalci da daidaito, kuma ginshiƙin cigaban dimokiraɗiyyar Nijeriya.”
- An Nuna Nezha 2 A Zama Na Musamman A Hedikwatar MDD Dake Birnin New York
- Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabuwar Rundunar Tsaro A Jihar
Ministan ya jaddada irin gagarumar gudunmawar da marigayin ya bayar a fannoni daban-daban, sannan ya ce irin rawar da ya taka a harkokin siyasa, kishin ƙasa, da zamantakewa ta bar tarihi mai kyau a tafiyar da mulki, haɗin kai, da cigaban ƙasa.
Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”
Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a.
“Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.