Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), ta ayyana yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 18 ga watan Fabrairu, saboda rashin magance musu wasu bukatun more rayuwa da suka bukata.
Kungiyar ta sanar da matakin ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Dr.Peter Adamu da sakataren kungiyar Dr. Peter Waziri, a ranar Talata.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alhinin Rasuwar Dattijon Kasa, Edwin Clark
- Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan amincewar majalisar zartaswar kungiyar ta kasa.
“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025.
“Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp